Dokar hana kiwo ba za ta yi tasiri ba – Zulum

Zulum ya yi alkawarin taimaka wa jami’an tsaro -A kowane lokaci

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum

Tura wannan Sakon

 Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce, dokar hana Fulani makiyaya yawo da dabbo­bin su ba za ta yi aiki ba a wad­ansu jihohin kasar saboda halin da ake ciki.

Zulum ya ce, abin da zai sanya dokar ta yi tasiri kamar yadda ake bukata, shi ne magance matsalolin tsaron da ake fama da su yanzu haka da kuma matsalar tattalin arzikin da ta addabi jama’a.

Gwamnan ya ce, ya zama wajibi a shawo kan matsalolin siyasa da na tatatlin arzikin da suka shafi jama’a saboda illar da talauci ta yi a Yankin Afir­ka ta Yamma abin da ke haifar da matsalar tsaro.

Zulum ya ce, ana ci gaba da samun matsalar karancin abinci kuma yana da cikin matsalolin da ke haifar rikice rikice, abinda ya sa gwam­natin jihar Borno ta kwashe shekaru 2 tana gabatar da bukatar ganin manoma sun koma gonakinsu domin gu­danar da harkokinsu.

Gwamnan ya kuma ce, bayan wadannan, akwai batun sasanta manoma da makiyaya da ke da matukar muhimman­ci domin ganin sun fahimci juna da sanin irin gudumawar da kowane bangare daga cikinsu ke bayarwa domin sa­mun zaman lafiya da rayuwa mai inganci.

Saboda haka Zulum ya ce, dokar da wadansu gwamnoni ke barazanar fara aiki da ita ba za ta yi tasiri ba, har sai sun zauna sun shawo kan wadan­nan matsaloli da ya ambata.

A farkon makon nan, gwamnoni 17 da ke kudancin Nijeriya suka sanar da cewa, daga ranar 1 ga watan Satum­ba, 2021 mai zuwa za su fara aiwatar da dokar hana yawon kiwo a jihohinsu baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *