Domin cike gurbin Eriksen: Man-United ta yiwo aron Sabitzer daga Munich

Tura wannan Sakon

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta karbi aron Marcel Sabitzer daga Bayern Munich wanda zai zauna Old Trafford har zuwa karshen wannan kakar.

Dan wasan tsakiyar na Austria mai shekaru 28 zai maye gurbin Christian Eriksen ne da ke fama da doguwar jinya da kuma Scott Mc Tominay da shima ya samu rauni a baya-bayan nan

.

Sabitzer wanda Munich ta sayo daga RB Leipzig lokacin ya na matsayin kyaftin wasanni 54 ya dokawa kungiyar ta Bundesliga daga sayensa a 2021 zuwa yanzu.

A jawabinsa bayan rattaba hannu kan yarejejeniyar zaman aron a tawagar Eric ten hag, Sabitzer ya ce amsa tayin zuwa Old Trafford matsayin aro ne saboda yasan cikakkiyar dam ace gareshi ya bayar da gudunmawarsa ga kungiyar. A tsawon lokacin da ya shafe yana taka leda a lig-lig din turai anga fuskar Sabitner sau 443 a filayen wasa yayinda a bangare guda ya dokawa kasarshi wasanni 68 tare da cin kwallaye 12.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *