Domin dakile ta’addanci: Zamfara ta horar da jami’an tsaron sa-kai

Gwamnatin Zamfara ta kaddamar da shirin horas da sababbin zaratan jami’an tsaron sa-kai da ta dauka domin dakile hare-haren ‘yan bindiga a karkashin kungiyar CPG a takaice. Bayanai na nuni da cewa, an zabo jami’an tsaron na CPG ne daga dukkanin masarautu 19 da ke fadin jihar.
Yayin da yake jawabi a wajen taron kaddamar da aikin horas da sababbin jami’an tsaron, gwamna Bello Matawalle ya sha alwashin aiwatar da karin matakan yaki da ta’addanci a jiharsa, la’akari da mummunan halin da ‘yan bindiga suka jefa dubban mutane musamman a yankunan karkara.
A makon da ya gabata gwamnatin Zamfara ta sanar da yanke shawarar bai wa al’ummar jihar damar mallakar bindigogi domin kare kansu daga ta’addancin ‘yan bindiga.
Zamfara da ke kan gaba a tsakanin jihohin Arewacin Najeriya masu fama da hare-haren ‘yan bindiga, a baya mahukuntan jihar sun sha yunkurin kulla yarjejeniyar sulhu da ‘yan ta’addan, amma lamarin ya ci tura.