Duk abin da mutum ya samu, silarsa Allah -Ogan boye

Yusuf Imam Ogan Boye
Daga Alhussain Dakace Zariya
Tun lokacin da aka bai wa Sanata Rufa’i Sani Hanga, takarar sanatan Kano ta tsakiya bayan ficewar Sanata Ibrahim Shekarau, daga NNPP wannan ta sa aka yada jita-jitar cewa, matasa masu goyon bayan Yusuf Imam Ogan Boye suka lalata hotunan dan takarar shugaban qasa na NNPP kuma madugun Kwankwasiyya, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso suka fusata na rashin bai wa Ogan Boye takarar Sanatan.
A kan haka ne Ogan Boye ya shaida wa manema labarai cewa, shi ba s hi da labarin lalata hutunan Kwankwaso domin kwanan sa daya da shigowa Kano, amma duk da haka zai bincika ya ji gaskiyar labarin.
Game da matsayinsa na takaran Sanata ya tabbatar wa da manema labarai cewa, duk wani abu da mutum ya samu daga Allah ne , saboda haka duk abin da ya samu ko ya rasa haka Allah ya qaddara.
Daga qarshe, ya shawarci ‘yan Kwankwasiyya da su zamanto masu kiyaye doka da oda da kuma gujewa duk wani abu da zai kawo rudani.