Duk da matsalar tsaro: An samu daukaka a fannin ilimi a Batsari -Dokta Salisu Garba

Daga Rabiu Sanusi Katsina
Karamar hukumar Batsari wadda ke yammacin jihar Katsina, kuma ta yi iyaka da kananan hukumomin Jibia da Safana, sai daga yamma kuma ta kasance mahada da jihar Zamfara.
Batsari ta na daya daga cikin kananan hukumomin da su ke fama da matsalar tsaro da masu garkuwa da satar shanu da jihar Katsina ke fama da shi.
Wannan kuma na daya daga cikin matsalolin da su ka kawo tarnaki a cikin al’amarun da ke wakana a yanki.
Amma kuma hakan bai wa gwamna ciwon kai ba, domin nemo hanyar da ya kamata a taimaka al’ummar wannan yanki ba da ilimi domin tsamo su daga kangin da su ka tsinci kansu.
Tashin farko gwamna Aminu Bello Masari ya yunkura da kansa ya zuwa yankunan da ke fama da wannan matsalar tare da kafa kwamitocin da za su taimaka masa, dan gano asalin abin da ke sa garkuwa da mutane da sace shanun al’umma.
Cikin ikon Allah kwamitin ya gudanar da aikin sa cikin natsuwa tare da tabbatar da rashin ingantaccen ilimi ga mazauna yankunan garin da makwabtansu.
Sannan kuma aka gana da ma su rike da wadannan yankuna kama daga dagattai, hakimai shuwagabanin Fulani da dukkan ma su ruwa da tsaki da kara tantance bukatunsu.
Cikin ikon Allah akai dukkan mai yiwuwa tare da sama masu makarantu da gyara masu da yawan wadansu da ke da bukatar hakan.
Dokta Salisu Garba matsayin shugaban ilimi na bai daya a karamar hukumar Batsari ya tabbatar ma da wakilinmu ci gaban da aka samu a zuwan gwamnatin gwamna Aminu Bello Masari, a cikin shekaru biyar da take rike da jihar.
Sannan mun kuma zagaya da shi makarantu domin ganin yadda tsarin koyarwa ke tafiya tare da tabbatar da ganin ko malamai suna aikinsu.
Bayan haka kuma akwai wadansu daga cikin gyare-gyare da gwamnati ta yi wa karamar hukumar ta Batsari cikin ikon Allah an samu nasara.
Sakataren ya kuma cewa, lallai babu abin da ya dace da ayyukan da ake gabatarwa na samar da ilimi face godiya ga gwamnati.
Sannan ya hori malamai da su kara tsare ayyukansu domin ganin sun sauke nauyin da Allah madaukakin sarki ya dora masu.
Haka zalika ya ce, idan za a tsaya lissafin ayyukan gwamna to babu lokacin gamawa, domin kuwa ya bada mahimmanci kwarai dagaske a fannin ilimi kamar yadda ya dauki alkawari.
Ya kuma yaba da irin yadda iyayen kasa suke ba su shawarwari a kan gudanar da ayyukansu da kuma tsawatarwa ga dukkan wata matsala da zata ta so.
Sai mazauna yankunan da matsalar tsaro ta yi kamari da ya bukaci hadin kansu ta re da fatan za su bar yaransu, su samu ilimi wanda zai kawo sauyi a rayuwarsu.
Dokta Salisu ya mika godiya ga dukkan mahukunta na sashen ilimin bai daya na jihar katsina, musamman shi mai girma ciyaman na Subeb Alh, Lawal Buhari Daura bisa namijin kokarin shi na kulawa da aikin shi.