Duk da tabarbarewar tattalin arziki: Masari ya yi ba-zata

A Katsina: Shirin basda ya inganta ilimi a jihar

A Katsina: Shirin basda ya inganta ilimi a jihar

Tura wannan Sakon

Hakika Dallatun Katsina Mutawallen Hausa gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya taka rawar gani a duk fadin jihar, saboda ya ba za ayyukan raya kasa duk da ya karbi jihar cikin matsanancin hali na tattalin arziki a kasar da matsalar tabarbarewar tsaro a wadansu sassa na Arewacin kasar, musamman jihohi da wadansu kananan hukumomi kamar wurin da nike shugabanta domin bani samun isasshen barci a watannin da suka gabata, in ji Alhaji Yahaya Yusuf Sani, shugaban karamar hukumar Batagarawa.

Harkokin gina al’umma ta fannin tallafi domin ya zama jari su dogara da kawunan su maigirma bunkasa harkar ilimi a jihar tun daga matakin makarantun firamare da sakadare dana gaba da sakandare ya gyara masu bukatar hakan kuma ya gina sabbi a dukkan wuraren da a ke bukatar hakan.

Ba anan abin ya tsaya ba saboda ta fuskar addini an gina makarantun Islamiyyu da gyara wadanda suka lalace an gina sababbi kuma an bayar da tallafi domin ginawa da kuma gyara ga wadansu.

Akwai wuraren da aka gina masallatai na kamsu salawati dana Juma’a wadanda ake bukatar a yi masu gyara suma an yi masu. Abinda ya shafi ilimi na addini da na sana’a watau na zamani sun samu kula wa yadda ya kamata.

Bala Garba Tsanni ya ce, ba jiyau ba ne shi ganau ne, ya shaida ire-iren ayyukan alheri da gwamna ya yi masu a karamar hukumar Batagarawa ya magance masu matsalar ambaliyar ruwa da zaizayar kasa da suke barazana ga muhallan su duk lokacin damina, ba kamar garin Kayauki da ya dade yana fuskanta matsalar, amma yanzu ya zama tarihi.

An yi hanyoyi da kwaltoci da magudanun ruwa shi kuma ruwan da ke gudanyowa an yi matara wuri daya domin jama’a su amfana da shi ta hanyoyi daban-daban, musamman noman rani su yaki talauci su bunkasa hanyar samun abin dogaro da kai a bar zaman kashe wando.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *