Duk da tsadar taki: Manoman Kano za su wadata kasa da abinci –Rahoto

Duk da tsadar taki: Manoman Kano za su wadata kasa da abinci –Rahoto

Noman Masara

Tura wannan Sakon

Daga Jabiru Hassan

Binciken da wakilinmu ya gudanar a sassa daban-daban na jihar Kano, ya nuna cewa, manoman jihar suna gudanar da aikace-aikace a gonakinsu duk da cewa, babu wadataccen taki mai rahusa wanda gwamnatoci ke samarwa ga manomansu kamar yadda aka saba.

Wakilinmu ya gano cewa, a wannan daminar, manoman sun rage noma kayan amfanin gona da suke da matukar bukatar taki kamar masara inda mafiya yawan kayan amfanin gonar da manoman suka shuka ba su damu da taki sosai ba.

Haka kuma a wadansu sassan jihar Kano musamman guraren da suke da gonaki masu ajiye ruwa manoman yankunan sun shuka shinkafa inda akalla idan kaka ta yi ko shakka babu za a sami yalwar shinkafa fiye da kowace shekara.

A shiyyar aikin gona ta daya da ke Rano, Albishir ta ziyarci garuruwan Kiru da Karaye da kuma kwanar Dangora inda wakilinmu ya zanta da wadansu manoman yankin inda suka bayyana cewa, daminar bana tana da tsafta da kuma albarka duba da yadda ake samun ruwa sosai ba tare da dogon tsaiko ba.

Sannan a shiyyar Dambatta manoman daga karama hukumar Dawakin Tofa da Makoda da kuma Ungogo sun sanar da cewa, rashin taki mai sauki ya sanya suka rage shuka masara a gonakin su amma sun zuba shinkafa da gero da kuma dawa harma da kayan lambu irin su tumaturi da albasa da kuma nau’in wake.

Su ma manoman shiyyar Gaya sun nuna cewa, taki ya yi tsada dole ta sa suka canza abubuwan da suke shukawa tare da yawaita sanya gero da ridi da sauran abubuwa kuma gonaki sun yi kyau sosai kamar yadda aka saba, inda mafiya yawan manoman da suka yi magana, sun roki gwamnatin Kano da ta samar da takin zamani mai sauki domin tabbatar da nasarar wadata kasa da abinci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *