Editoci sun yi babban taro -Karo na 18

Editoci sun yi babban taro -Karo na 18

Editoci sun yi babban taro -Karo na 18

Tura wannan Sakon

Aliyu Umar daga Owerri

A ranar Alhamis da ta gabata,10 ga Nuwamba 2022, aka fara babban taron kungiyar Editocin Nijeriya (NGE), a garin Owerri, babban birnin jihar Imo.

Taron mai taken; Dandalin siyasa, zabe na gaskiya da rawar da Editoci za su taka, ya sami halartar gwamna jihar Imo, Sanata Hope Uzodinma da dukkan mukarrabansa. Tsare-tsaren taron ya nuna cewa, bayan bude taron, ta hannun gwamna a rana ta farko, a rana biyu an ci gaba da shi bisa jagorancin Uwargida Ibim Semenitari.

Har ila yau, babban mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaro, Janar Babagana Monguni, wanda zai nusar da editoci kan harkar tsaro ya sami wakilcin wani jami’insa.

A rana ta uku kuma ta karshe, babban manaja kuma babban editan jaridar Banguard, Yarima Gbenga Adefaye, ya jagaranci hidimomin da taron ya yi. A ranar Lahadi,13 ga Nuwamba 2022 aka kawo karshen taron, kowa ya koma garin da ya fito.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *