Farawa ya taya al’ummar Musulmi barka da Sallah

Alhaji Hassan Garban Qauye Farawa,

Tura wannan Sakon

Daga Mahmud Gambo Sani

Shugaban qaramar hukumar Kumbotso Alhaji Hassan Garban Qauye Farawa,ya taya al’ummar Musulmi farin ciki bisa kammala ibadar azumin Ramadan na bana da bukukuwan Qaramar Sallah lafiya.

A sanarwar da mai taimaka masa kan harkar yaxa labarai Shazali farawa ya sanya wa hannu aka raba wa manema labarai ya ce, shugaban ya bukaci musulmai da su yi amfani da wannan lokaci na bukukuwan sallah wajen yin addu’o’in samun zaman lafiya ga qasa gaba daya musamman kan karuwar rashin tsaro da matsalar tattalin arziki.

Shugaban ya kuma mika sakon barka da Sallah ga gwamna Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje da shugaban riko na jam’iyyar APC, Alhaji Abdullahi Abbas Sunusi da kwamishinan ma’aikatar qananan hukumomi, Alhaji Murtala Sule Garo da majalisar masarautar Kano da kuma al’ummar Musulmi baki daya musamman na qaramar hukumar Kumbotso.

Garban Qauye ya yi kira ga al’ummar qaramar hukumar Kumbotso da su ci gaba da aiki tuquru wajen samar da zaman lafiya da ci gaba da kwanciyar hankali musamman a tsakanin al’ummar qaramar hukumar ta Kumbotso da jiha gaba xaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *