Farfesa Isah Pantami, kogi matattarar ilimi -Farfesa Rasheed

Farfesa Isah Pantami, kogi matattarar ilimi -Farfesa Rasheed

Farfesa Isah Pantami

Tura wannan Sakon

Daga Danjuma Labiru Bolari, Gombe

Babban sakataren hukumar kula da manyan jami’oin Nijeriya, Farfesa Abubakar Adamu Rasheed, ya bayya­na Farfesa Isa Ali Pantami, a matsayin kogi matattarar ilimi bisa ga bai wa da fiki­rar da Allah ya yi masa.

Farfesa Abubakar Ra­sheed, ya bayyana hakan ne a wajen wani taro na mataimakan shugabanin jami’oin gwamnati na Nijeriya da aka gudanar a babban birnin tarayya Abuja a ranar 21 ga watan Yuli na wannan shekarar, ya ce, ya jinjina wa Farfesa Pantami a kan bai warsa.

Ya ce, ya san Farfe­sa Isah Ali Pantami, so­sai haziki ne domin akwai wata rana da za’a yaye dalibai a jami’ar tarayya ta garin Minna, shugaban Nijeriya Muhammad Bu­hari, ya tura shi ya wakilce shi amma ganin Pantami na garin a lokacin ya ce, shi yafi da cewa, ya wakilci shugaban kasa a matsayin sa na ministan Najeriya.

“ A wakilcin na Pantami ya cika da mamaki domin yadda ya gabatar da maka­la a wajen kowaye ne iyaka kenan”

Farfesa Rasheed, ya kuma ce wata rana Dansa ya gaya masa cewa yana mamakin Pantami, idan ya karanta takarda sau daya sau biyu duk yawan ta zai hadda ce ta.

Ya kara da cewa, tun ka­fin ya zama Farfesa Isa Ali yake da bai wa ta musam­man har zuwa yanzu da ya zama Farfesan Farfesosi.

A cewarsa, ba kowane Farfesa ne zai yi kamar Pantami ba domin haka daga yanzu ya zama Dis­tingushed Professor.

Ya ci gaba da cewa, a makalar da Isah Ali ya gabatar kowa ya kwank­wadi ilimi ya koshi domin ya fito da tsari na zamani kan tsare-tsaren darussan da ake koyarwa a jami’oin kasar nan zuwa hanya ta zamani.

Sakataren, ya yi amfani da wannan damar ya kara jinjina wa Farfesa Isah Ali Pantami kan makalar da ya gabatar da ka ba tare da wata takarda a hannu ba duk wanda ya halarci taron ya san Farfesa ya ma wuce kogin ilimin.

Sannan sai ya hori shugabanin jami’oin da cewa, su tattara bayanan Pantami waje guda a buga ko a tura wa mutane kai tsaye domin su rinka naz­ari a kai suna kara samun ilimi.

Daga nan sai ya ce, kowane Malami a jami’a yana alfahari da daliban sa masu hazaka amma shi Farfesa Pantami daliban ilimi ne a ko’ina suke al­fahari da shi.

A b angaren bunkasa tattalin arziki ta hanyar sadarwar zamani babban darakta na Galady Back bone, Farfesa Muhammad Bello Abubakar, ta bakin maitaimaka masa a b angar­en sadarwa Tasiu Moham­mad Pantami ya ce, arzikin Nijeriya ya bunkasa sosai

Ya ce, Isah Ali Pantami, minista ne da ba’a tab a yin kamarsa a tarihin Nijeriya, kuma ya bar tarihin da ba za a tab a mantawa da shi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *