Fatanmu, Hada Kan ‘Yan Nijeriya A Zabi Tinubu – Rabi Dangizau

Tura wannan Sakon

Daga Babangida S Gora, Kano

An bukaci ‘ya’yan kungiyar (PAPSA) tun daga matakin kasa har mazabu da su kara zage damtse domin ganin dan takarar shugabancin kasar nan karkashin jam’iyyar APC, Asuwaju Bola Tinubu ya sami nasarar lashe zabe mai zuwa na 2023.

Kiran ya fito daga bakin Ambasada Rabi, wadda ita ce babbar daraktar kungiyar wayar wa da jama’ar Kudu da Arewa kai kan mahimmancin zabar Tinibu domin ya dora daga inda shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya tsaya da ayyukan bunkasa kasa.

Rabi ta yi wannan kiran ne yayin gabatar da shugabannin kungiyar ta (PAPSA) a dakin taro na Ni’ima Guests Palace da ke unguwar Nassarawa GRA, a jihar Kano.

 Ambasada Rabi ta ce, yadda ta san Asuwaju Bola Ahmadu, mutum ne da bai da kabilancin yare ko addini, kuma babu ruwansa da dukkan wani bangaranci, sannan kuma ta nuna irin taimakon al’umma da yake yi a yanzu ya sa kungiyoyi suka fito domin mai da bikin alkhairi da ya yi masu a lokacin zaben da ke zuwa.

 Ta kuma bukaci matasa maza da mata da su bayar da hadin kai wajen dukkan ’yan takarar da ke karkashin jam’iyyar APC domin ganin sun sami nasara a zabe mai zuwa.

Sannan ta bukaci ’yan kungiyar da su tabbatar da sun mallaki katin zabe domin da shi ne za a sami nasarar zaben.

A nasa jawabin, kakakin jam’iyyar APC na jihar Kano, Honarabul Ahmad Aruwa, ya ce, wannan ba abin mamaki ba ne kasnceFatanmu, hada kan ‘yan Nijeriya a zabi Tinubu -Rabi Dangizau war gwamna Abdullahi Umar Ganduje tuni ya fara dawainiya ga tafiyar Tunibu.

Ya ce, lallai kiran da wannan kungiya ta PAPSA ta yi masu tare da karrama shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, da shi kansa ba abin wasa ba ne abu ne mai mahimmanci, kuma wannan tafiya ta kungiyar irinta ake so kuma ake bukata.

Aruwa ya ce, lallai yanzu lokaci ne na canza abubuwan da ake ganin wasu sun bata, amma Tinibu ya zo zai kawo gyara domin shi mutum ne da ya sha bamban da sauran ’yan siyasa Daga karshe kakakin jam’iyyar ya bukaci sauran bangarorin siyasa da su kasance ma su jan kunnen mabiyansu domin yin siyasa mai tsabta ba tare da tayar da hankali ko tarzoma ba, kasancewar duk sunansu Kanawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *