Fifikon gwamnatin Buhari, samar da tsaro – Lai Mohammed

Fifikon gwamnatin Buhari, samar da tsaro - Lai Mohammed

Lai Mohammed

Tura wannan Sakon

Daga Mahmud Gambo Sani

Ministan yada labarai da al’adu na kasa, Alhaji Lai Mohammed ya jaddada kudirin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari na ganin ta magance matsalar tsaro da ta addabi kasar.

Ministan ya bayar da tabbacin ne a lokacin da yake jawabi a wurin taron bita na kasa na yini biyu kan gudummawar da kafafen yada labarai za su bayar kan al’adu, zaman lafiya da kuma tsaron kasa wanda cibiyar wayar da kan al’umma kan al’adu ta kasa watau National Institute for Cultural Orientation (NICO) ta shirya, aka gudanar a Cibiyar Nazarin Harkokin Dimukuradiyya ta jami’ar Bayero, da ke gidan Mumbayya, unguwar Gwammaja cikin birnin Kano.

Mohammed wanda darakta a ma’aikatar, uwargida Maimunatu ta wakilta, ya ce, baya ga makudan kudaden da gwamnati ta zuba a harkar tsaro wajen sayo makamai, shugaban kasa ya dada tura kudurai guda biyu ga majalisar kasa wanda ya kunshi kudirin takaita bazuwar abubuwan fashewa da kuma kudirin takaita bazuwar manya da kananan makamai a kasa.

Ya karfafa cewa, yaki da ta’addanci da kuma rashin tsaro ba na gwamnati ne kadai ba, ya kamata kowa ya sa hannu a ciki idan har ana so a ci galabar yakin kuma ana so a sami ci gaban kasa.

Ya kuma yaba sosai da irin gudummawar da kafafen yada labarai suke bayarwa wajen yada labaran gaskiya domin samar da tsaro da ci gaban kasa, inda ya kuma hore su da su kauce wa labaran karya da labaran tunzurarwa wadanda suke illa ga tsaro da zaman lafiya da ci gaban kasa.

Daga nan sai ya roki ‘yan jarida da kafafen yada labarai da su sanya kishin kasa a gaba wajen gudanar da aikinsu la’akari da damar da kundin tsarin mulkin kasa ya ba su da kuma ka’idojin aikinsu.

Daga karshe, ya yaba wa cibiyar ta NICO wadda take hukuma ce a karkashin ma’aikatar ta yada labarai da al’adu bisa kokorinta a kowace shekara na shirya irin wadannan bitoci domin wayar da kan al’umma kan muhimmancin al’adu bisa kasancewarsu kashin bayan ci gaba da kuma wayar da kan al’umma kan zaman lafiya da gujewa tashin hankali domin samar da ci gaban kasa.

Tun da farko da yake jawabi, sakataren zartarwa na cibiyar, Ado Mohammed Yahuza, ya ce, cibiyar ta shirya taron ne domin wayar da ’yan jarida kai da sauran jama’a kan taka rawar da za su iya yi wajen samar da zaman lafiya a kasa.

Ya kara da cewa, bitar za ta koyar da ‘yan jarida yadda za su sanya kishin kasa a lokacin da suke aikinsu wajen guje wa rubuta labaran kanzon-kurege da kuma mayar da hankali wajen rubuta abin da zai kawo hadin kan kasa da dankon zumunta a tsakanin al’ummar kasa.

A nasa jawabin, shugaban kungiyar ’yan jarida na jihar Kano, Malam Abbas Ibrahim ya bayyana cewa, ’yan jarida suna da gagarumar gudummawar da za su bayar wajen samar da zaman lafiya da ci gaban kasa, inda ya hori ‘yan jaridar da su mayar da hankalinsu wajen yada labaran da za su samar da zaman lafiya da ci gaban kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *