Fifita karatun boko kan na addini, ina mafita?

Tura wannan Sakon

Daga Dokta Saidu Ahmad Dukawa Buk

Jawabin azumi na makarantar Manar-elhuda Taken maudu’in zai sa a zaci za a koka ne game da yadda Musulmi a yau suka fi fifita karatun boko a kan na addini a yayin kokarin ilimantar da ‘ya’yansu.

Ko shakka babu wannan babbancin a bayyane yake, ba kawai a mataki na daidaikunmu ba, amma har a hukumance. Alal misali, an ware lokuta mafiya tsada an kevewa makarantun boko, tun daga sanyin safiya har goshin la’asar yara suna makarantun boko ne, sai bayan sun dawo a gajiye, sannan za su sauya shiga su tafi makarantar addini, ga wadanda suke zuwa makarantar addinin kenan.

Haka kuma hukomominmu suna ware kasafin kudi ne kadai ga makarantun boko, a mafi yawan lokaci. Bayan samar da gine-gine, da daukar malaman boko da biyansu, da samar da kayan koyo da koyarwa, da filayen motsa jiki, da sauran abubuwa na larura, har abinci ake bai wa yara ‘yan makarantar boko da nufin a ja hankulansu zuwa makaranta.

Makarantun addini kuwa ko oho! Hasali ma, wadansu makarantun kamar na allo bin su ake yi ana fafararsu, saboda kyama da wadansu ‘yan bokon suke yi masu. Haka kuma a daidaikunmu za ka ga muna fafutukar biyan kudin makarantar boko a kan kari, amma na makarantar addini tare da karancin kudin sai an yi ta artabu da mu.

Wadansu ma ba sa saka ‘ya’yansu a makarantar addini gaba daya ma! Na tuna wani uban yara da na tava bai wa shawarar saka ‘ya’yansa a wata makarantar addini ya ce, a bari su yi candi tukunna (watau su gama sakanadare) domin kada a rarraba masu hankali, ya ce, karatun boko yana da lokaci, yayin da na addini yake nan har tsufa.

A karshe, ‘ya’yan na sa sun yi ilimin boko har matakin jami’a amma ban ga alamar suna yin karatun addini kowane iri ba.

Haka kuma sau da yawa muke ganin manyan jami’an gwamnati suna halartar bita iri daban-daban har zuwa ritayarsu, sai daga baya ka ji suna neman wurin da za su samu ilimin addini. Masu sukuni a cikinsu har kasar suke bari, su tafi irin su Sudan ko Misra, da nufin koyo harshen larabci, wai ko sa samu su iya karatun Al-kur’ani. Duk irin wadannan misalan suna nan.

Amma a fahimta ta, zai fi mana kyau mu yi waiwaye adon tafiya mu ga ya ya lamari yake tun farko a duniyar Musulunci? Kuma yaushe al’amura suka sauya? Sannan ya ya za a yi a dawo kan turba?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *