Filin da Kogi ta mallaka wa BUA: Kamfani ya ce, a kai kasuwa

Daga Mahmud Gambo Sani
Kamfanin BUA mallakin Abdussamad Isyaku Rabi’u ya bayyyana cewa, ba ya bukatar fili kadada dubu 50 da ya saya a jihar Kogi a shekara ta 2012 domin gina masana’anta saboda rashin ingancinsa.
Wata wasika da kamfanin ya rubuta wa gwamnatin jihar Kogi wadda ta yi barazanar kwace filin, ta ce, kamfanin ya bayyana dalilan da suka sanya shi kasa gudanar da aiki a filin tare da kin biyan kudin mallakarsa.
Kamfanin BUA ya ce, matsalar tsaro da rashin hanya da kuma rashin kayan more rayuwa na daga cikin dalilan da suka sanya shi sake tunani a kan mallakar filin da ake takaddama a kai.
Wasikar ta ce, tun bayan da kamfanin ya amsa gayyatar zuba jari a jihar Kogi a shekarar 2012, babu wani yunkuri da gwamnatin jihar ta yi wajen samar da hanya ko kayan more rayuwar da zai karfafa masa amfani da filin kamar yadda suke bukata.
BUA ya ce, yanzu haka babu hanyar zuwa filin da ake magana a kai sai ta cikin ruwa, kuma matsalar tsaro a wurin ta sa ba za su iya zuba jarinsu a filin ba kamar yadda suke bukata. Kamfanin ya ce, binciken masana da suka yi a filin ya nuna masu cewa, kashi 30 ne kawai na filin ke da inganci, yayin da kashi 66 duk duwatsu ne da tsaunuka wadanda ba za su ba su damar gudanar da aikin da suke bukata ba.
Saboda wadannan dalilai, kamfanin BUA ya shaida wa gwamnatin jihar Kogi cewa, baya bukatar filin kuma sun dakatar da shirin zuba jarin da suke da shi a wurin.
Kamfanin ya ce, da filin ya cika muradunsu da tuni sun biya shi kafin fara duk wani aiki kamar yadda manufofinsa yake a ko’ina, saboda haka gwamnatin jihar Kogi na da hurumin soke takardar mallakar filin ba tare da wani haufi ba.
Wannan takaddama na BUA da gwamnatin jihar Kogi na zuwa ne kasa da mako guda bayan wadda aka fara tsakanin gwamnatin jihar da kamfanin simintin Dangote wanda ya kai ga rufe kamfanin da ke Obajana.
Kungiyar ‘yan-kasuwa da masu zuba jari a Nijeriya tare da masana tattalin arziki na bayyana damuwa a kan wannan dambarwa wadda ke barazana ga ayyukan jama’a da kuma shirin zuba jari a Nijeriya.