Fina-finan fasadi: Kasar Makka ta nuna wa Netflix yatsa

Fina-finan fasadi: Kasar Makka ta nuna wa Netflix yatsa

Netflix

Tura wannan Sakon

Kasashen Larabawa na yankin kogin pasha sun nemi kamfanin Netflix ya cire dukkan fina-finan da suka sabawa dokokin Musulunci.

A wata sanarwa da kungiyar kasashen yankin kogin pasha ta fitar ta yi gargadi cewa, wadansu fina-finai na baya-bayan nan da aka yi domin yara sun saba wa dokokin Ubangiji.

Sai dai ba a yi wani karin bayani ba, amma duk da haka kafar telebijin ta kasar Makka ta nuna bidiyon da aka dusashe fuskarsu na katun din fim din Jurassic World: Camp Cretaceous, wanda aka nuna wadansu yara mata biyu suka nuna suna son juna tare da sumbatar juna.

Gidan telebijin na Al Ekhbariya da ya nuna wani sashe na fim din da wani kamfanin Faransa na Cuties ya shirya, ya sanya take kamar haka “bidiyon da ke nuna rashin da’a da rusa tarbiyya wanda ke barazanar lalata tarbiyyar yara.”

A wani bidiyon da Al Ekhbariya ta wallafa a shafinta na intanet ta yi zargin cewa, fim ɗin yana yaɗa luwaɗi da maɗigo.

Kazalika gidan telebijin ya yi hira da mutane da dama da suka yi irin zargin tare da kiran hukumomi su ɗauki mataki cikin gaggawa.

An tuntuɓi Netflix da ya cire bidiyon, da kuma duk wadansu fina-finai da aka shirya domin yara, tare da tabbatar da bin dokoki,” kamar yadda sanarwar hadin gwiwa daga hukumar kula da fina-finai ta kasar Makka da ta kulla da kafafen yada labarai.

Hukumomi za su sanya ido domin ganin ko an bi umarnin, tare da daukar matakan shari’a idan har aka ci gaba da yada fina-finan”, kamar yadda suka yi gargadi.

Babu wani martani daga kamfanin Netflix.

Duk da cewa, kasar Makka ba ta da wadansu dokoki na damar zabar jinsi, amma yin luwadi da madigo da zina haramun ne a kasar. A karkashin dokokin Musulunci na kasar, hukuncin duk wanda aka kama da laifin luwadi ko madigo hukuncinsa shi ne kisa ko bulala

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *