Fulani, Yarabawa yan-uwan Juna- Tinubu

Daga Mahmud Gambo Sani
Jagoran jam’iyyar APC na kasa , Bola Ahmed Tinubu, ya ce ya zabi jihar Kano a matsayin wurin da za a gudanar da taron tunawa da ranar haihuwarsa karo na 12 da kuma cikarsa shekara 69 domin tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa Yarbawa da Fulani kansu a hade yake.
Tinubu, wanda ake kyautata zaton cewa ya fara nuna bukatarsa ta neman kujerar Shugabancin kasa, ya bayyana cewa, aurar da ‘yar Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje; ga dan tsohon gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi, wanda aka yi a Kano a shekarar 2018 cikkakkiyar shaida ce ta hadin kan kasa.
Jagoran jam’iyyar APC na kasa ya kuma yi tir da yunkurin wasu marasa kishin kasa na ganin hadin kan kasar ya wargaje ta hanyar tashe -tashen hankula.
“Me ya sa muka zo Kano? Domin mu nuna wa ‘yan Nijeriya a wannan mawuyacin lokaci da muke ciki cewa akwai wani bafulatani, makiyayi wanda ya bayar da ‘yarsa aure ga wani manomi, bayerabe , amma duk da haka har yanzu wasu mutane suna tayar da hankalin al’umma da sunan kabilanci, wannan ba daidai ba ne ” A cewar Tinubu