Gadar Muhammadu Buhari: Kano za ta kashe Naira biliyan 9

Gadar Muhammadu Buhari: Kano za ta kashe Naira biliyan 9

Gadar Muhammadu Buhari

Tura wannan Sakon

Daga Mahmud Gambo Sani

Majalisar zartarwa ta jihar Kano ta amince da fitar da kusan Naira biliyan 9 domin gina gagarumar gadar sama a shataletalen babban gidan man NNPC da ke Hotoro, a kan titin Maiduguri a cikin birnin Kano.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai kan sakamakon taron mako-mako da majalisar zartarwa ta jihar ta gudanar a dakin taro na Afirka House, da ke gidan gwamnatin jihar.

Ya ce, aikin na daga cikin kudurin gwamnatin Dokta Abdullahi Umar Ganduje na gina hanyoyi domin magance cunkoson ababen hawa a fadin birnin, da kuma tsarinta na sauya Kano zuwa babban birni na zamani domin bunkasa harkokin kasuwanci.

Malam Garba ya bayyana cewa, kasancewar Kano birnin da yake bunkasa kuma muhimmiyar cibiyar kasuwanci a cikin qasar, Kano tana samun karuwar masu shigowa domin yin kasuwanci saboda haka bukatar sake fasalin tare da inganta hanyoyin da ake da su domin bunkasa kasuwanci da inganta zirga-zirgar ababen hawa.

Kwamishinan ya kuma sanar da cewa majalisar ta amince da a kashe Naira miliyan 44, domin tantance kwasa-kwasai a Kwalejin aikin gona ta Audu Bako da ke Dambatta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *