Ganduje, a farfado da Inuwar Jama’ar Kano -Harisu Bello

Daga Jabiru Hassan
Al’umar jihar Kano sun yi kira ga gwamnan jihar Dokta Abdullahi Umar Ganduje da ya farfado da “Inuwar Jama’ar Kano” watau (Kano Forum) ta yadda zata ci gaba da gudanar da aiyukan ta kamar yadda aka sani tun kafa kungiyar.
Mafiya yawan mutanen da suka zanta da Albishir sun sanar da cewa ko shakka babu Inuwar Jama’ar Kano tana da muhimmancin gaske musamman irin rawar da ta taka a baya wajen tallafawa harkar ilimi da bunkasa yanayin koyo da koyarwa a fadin jihar Kano, tareda fatan cewa gwamna Ganduje zai duba wannan kira na al’umma kan wannan kungiya.
Malam Harisu Bello, wani malamin makaranta daga yankin karamar hukumar Dawakin Tofa, ya shaidawa wakilin mu cewa” zai yi kyau maigirma gwamna ya farfado da Inuwar Jama’ar Kano saboda muhimmancin ta ga al’umar jihar Kano musamman ta fuskar ilimi da kuma kyautata yanayin koyo da koyarwa, sannan wannan kungiya ta kasance abar alfaharin kanawa duba da irin aiyukan da tayi a baya na alheri” inji shi.
Shima wani tsohon jami’in ilimi a Kano Malam Isah Adamu yace farfado da Inuwar Jama’ar Kano abu ne maikyau kuma kowa yaga irin aiyukan da tayi wajen tallafawa harkar ilimi tun daga tushe, musamman ganin yadda many an mutane kuma masu martaba da rikon amana suke cikin wannan kungiya.
Wakilin mu wanda ya ziyarci babban ofishin kungiyar ta Inuwar Jama’ar Kano dake kan titin Lawan Dambazau ya ruwaito cewa anyi watsi da gine-ginen ofisoshin da aka fara a cikin hesikwatar kungiyar sannan babu wani aiki da aka gudanatwa domin ci gaban al’uma duk da cewa kungiyar tana da matukar muhimmanci.
Wasu ma’aikatan gurin da suka bukaci a sakaya sunayen su sun bayyana cewa ba’a komai a wannan guri kuma komai ya tsaya saboda rashin farfado da aiyukan wannan kungiya, sannan sunce akwai bukatar sake bunkasa ta da bats damar yin aiki kamar yadda manufifin kafata suke, tareda yin jinjina ga gwamantin Ganduje saboda kokarin da take yi wajen bunkasa jihar Kano ta kowane fanni.