Ganduje, garkuwar ilimi a jihar Kano -Garun-Danga

Daga Salihu S. Gezawa
An bayyana gwamnan jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje a matsayin garkuwar ilimin jihar Kano, bayanin ya fito daga bakin sakataren ilimi na qaramar hukumar Gabasawa Malam Kabiru Yusuf Garun-Danga, yake bayyana haka ga manema labarai inda ya ce babu tantama gwamna Ganduje gwarzo ne abin koyi a matakai daban-daban.
Malam Kabiru Garun-Danga ya ce tun a zangon farko na zuwan Ganduje ya yi abin a zo a gani wanda ya nuna a fili cewa, gwamnatin Ganduje da gaske take wajen raya ilimi wanda kowa ya yarda shi ne qashin bayan ci gaban kowace al,umma.
Garun-Danga ya ce babu abin da za su ce da gwamna Gandujen sai godiya da sambarka bisa ga cewa, duk da halin da tattalin arziqi ya shiga amma Ganduje bai gaza wajen bai wa ilimi fifiko ba, wanda kwana-kwanan nan Ganduje ya sahalewa daukacin qananan hukumomin jihar Naira milyan ashirin-ashirin da gyaran makarantun firamare ga kuma rabon kayan aiki da gwamnan ya yi duk da nufin ciyar da ilimin firamare gaba a fadin jihar.
Daga nan Garun-danga ya godewa shugaban hukumar kula da makarantun firamare ta jihar Kano Dokta Danlami Hayyo, saboda qwazonsa na ciyar da hukumar gaba.
Daga qarshe sakataren ilimin ya jaddada godiyarsa ga shugaban qaramar hukumar Gabasawa Alhaji Mahe Garba Garun-danga, saboda fifikon gaske da yake bai wa sashen ilimi na qaramar hukumar, haka kuma ya yabawa daukacin ma’aikatansa bisa hadin kan da suke bashi.
Ya yi kira ga malaman firamaren qaramar hukumar kan su qara himmatu wa wajen kula da ayyukansu tare da tsare amanar da aka ba su.