Ganduje, ginshikin ilimi, tauraron gwamnoni -Garun-danga

Daga Salihu S. Gezawa
An bayyana gwamnan jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, a matsayin garkuwar ilimi kuma tauraron gwamnonin Arewa.
Sakataren ilimi na karamar hukumar Gabasawa, jihar Kano, Malam Kabiru Yusuf Garun-danga shi ya yi batun, a lokacin da yake zantawa da manema labarai, inda ya ce, tabbas gwamna Abdullahi Umar Ganduje mikiya ne mai hangen nesa wanda ke da manufofi managarta da za su kai jihar Kano ga nasara.
Malam Kabiru Garun-danga ya ce, babu abin da jama’ar jihar Kano za su ce, sai godiya da sambarka domin Gandujen kanawa ya fitar da kanawa kunya wajen ayyukan raya kasa, da inganta lafiya, raya karkara da kuma uwa-uba gina ilimi ta hanyar bai wa makarantun firamare kulawar gaske.
Garun-danga ya ce, hakika gwamna Ganduje gwarzo ne abin koyi ta kowanne bangare tare da yin amfani da kwarewarsa wajen kawo ci gaban a zo a gani duk da yawan al’ummar jihar Kano.
Daga nan Garun-danga sai ya yi kira ga jama’ar jihar Kano da su ribanya goyon bayansu ga Khadimul Islam Ganduje wanda ya hana idonsa barci domin ganin jihar Kano ta kara amsa sunanta.
Da ya juya ga malaman firamare na karamar hukumar Gabasawa, kira ya yi gare su da su kara himmawajen sauke nauyin da Allah ya dora masu na bayar da ilimi da tarbiyya inda ya ce, su sani amana ce da Allah ya ba su kuma zai tambaye su gobe kiyama.
Ya kuma yi kira ga iyayen yara na karamar hukumar da su rinka ziyartar makarantun yankin domin ganin irin yadda harkar koyo da koyarwa ke tafiya. ya ce, harkar ilimi ta kowa ce, domin haka ya ce, akwai bukatar kowa ya shigo domin hada hannu da gwamnati wajen daga darajar ilimi a karamar hukumar da ma jihar Kano.
Daga nan ya gode wa shugaban karamar hukumar, Alhaji Mahe Garun-danga saboda goyon bayan da yake bai wa sashen ilimi na karamar hukumar.