Ganduje ya Kaddamar jami’an lafiya, a matakin farko

Tura wannan Sakon

Daga Wakilinmu

Gwamnan jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, ya kaddamar da jami’an lafiya a matakin farko kimanin 1,440 da suka hada maza da mata daga kananan huku­momi goma, an gudanar da bikin kaddamarwar a dakin taro na Coronation da ke gi­dan gwamnatin jihar, inda ya samu halartar manyan jami’an kula da lafiya da ke jihar.

Da yake gabatar da jaw­abinsa ga mahalarta taron gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce jami’an lafiyar za su rinka shiga gi­da-gida domin wayar da kan mata da masu juna biyu da kuma kananan yara yadda za su kula da lafiyar su.

Gwamnan ya ce wannan yunkuri ne na inganta lafi­yar al’ummar jihar.

A na sa jawabin babban sakataren kula da lafiya a matakin farko na jihar Dok­ta Tijjani Hussaini ya nuna farin cikinsa da kaddamar da shirin ya ce za a fara ne a kananan hukumomin jihar guda goma, za su taimaka wa mata masu juna biyu da kananan yara masu dauke da cutar zazzavi da sauran cututtukan da ke addabar kananan yara.

Dokta Tijjini Hussaini ya ce gwamnatin Kano tana kusanto da harkar lafiya ga al’ummarta ta yadda ba sai sun sha wata wahala ba wajen neman magani.

Shi kuwa daraktan lafiya mai kula da shiyyar Rano, Alhaji Bilyaminu G. Zubairu, ya nuna farin cikin­sa a kan wannan namijin ko­kari da gwamnan yake yi a kan harkokin lafiya a dauka­cin manya da kananan asibi­tocin jihar Kano.

Malam Bilyaminu G. Zubairu ya kara da cewa, hakan da gwmamnan ke yi yana bunkasa ci gaban ma’aikatan lafiya ta fannoni da dama. Ya bayar da misali da yadda a lokacin gwamna Ganduje ya kai matsayin manaja, duk inda aka kaishi domin warware matsaloli a kan harkar lafiya ya na sa­mun nasara.

Ba zai manta da mulkin Ganduje ba, domin yanzu har ya kai ga matsayin da­rakta mai kula da asibitocin shiyyar garin Rano, ba wani abu ya kai shi ga samun ci gaban ba sai kwatanta gas­kiya da amana tare da jajirce wa a kan aiki, tare da bai wa kowa hakkinsa na aiki.

Daraktan ya ce muka­man da yake samu zai kara masa kaimi wajen kula da aikinsa na harkar lafiya, sai ya yi kira ga ‘yan uwansa ma’aikatan lafiya na jihar Kano, da kasa baki daya cewa, su tsare gaskiya da amana.

Daga karshe ya na gode­wa Kwamishinan lafiya na jihar da kuma babban sakatare a hukumar lafiya a matakin farko na jihar Dokta Tijjani Hussaini da sauran manya da kananan ma’aikatan lafiya da ke ji­har.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *