Garkuwa: Zamfara ta kubutar da mutane 1,879

Alaka da ‘yan-fashi: Gwamnan Zamfara ya dakatar da sarkin Dansadau

Gwamnan Zamfara Bello Matawale

Tura wannan Sakon

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle ya bayyana cewa, bisa kokarin jami’an tsaro gwamnatin jihar ta ceto mutane 1,897 da ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane suka yi garkuwa da su a fadin jihar.

Matawalle ya bayyana haka ne a wajen bikin tunawa da sojojin kasar na shekarar 2022 da aka yi a Gusau makon da ya gabata. Ya yaba wa rundunar sojojin Nijeriya da ‘yan’uwansu a jihar bisa irin gudunmawar da ya bayyana a matsayin na musamman a kokarin dawo da doka da oda a jihar.

Ya ce“Na baya-bayan nan shi ne ceto mutane 97 daga sansanin Bello Turjis ba tare da biyan kudin fansa ba, ya ce, tuni dai wadanda abin ya shafa sun sake haduwa da iyalansu,” in ji shi.

Gwamnan ya bukaci sojojin da su gudanar da ayyukansu cikin dokokin cikin gida da na kasa da kasa wadanda ke jagorantar ayyukan tsaro ta hanyar tausayawa da mutunta duk wani domin kasa mai bin doka da oda. Ya bukaci masu ruwa da tsaki su tallafa wa jami’an tsaro da muhimman bayanai da za su taimaka wajen yakar miyagun laifuffuka a jihar, ya ce “Muna fatan ci gaba da yin aiki tare da ku doimn magance ƴan matsalolin tsaro da suka rage.

Da yake karin haske kan muhimmancin tunawa da ranar sojoji, Matawalle ya ce, gwamnati na bikin tunawa da sadaukarwar da tsofaffin da suka sadaukar da rayuwarsu domin ci gaba da zaman lafiya da hadin kan kasa. Ya kuma nuna jin dadinsa ga irin gudunmawar da rundunar sojojin kasar ta bayar wanda ya sanya Nijeriya ta taka rawar gani a taswirar duniya da ma sauran kasashen duniya fiye da shekaru 60.

“Haka zalika ya zama abin tunatarwa ga ‘yan kasar da su kaurace wa kalaman da ba a kiyaye ba, ayyukan rarraba kan jama’a da kalamai da ka iya kawo cikas ga hadin kai da ci gaban jiharmu da kasa baki daya,” in ji shi. Matawalle ya ce, gwamnatin jihar ta yi isassun shirye-shirye domin jin dadin jami’an da suka mutu a lokacin gudanar da ayyukan tsaron cikin gida.

“Ina jinjina wa kokarinku da kuma fatan jama’a su taimaka wa rundunar sojojin Nijeriya tare da gudummawar da suka bayar wajen tabbatar da zaman lafiya da gina kasar mu mai daraja,” in ji shi. Gwamnan a yayin taron, ya duba faretin sojoji, ya shimfida furen, ya kuma saki tantabaru a matsayin alamar hadin kai tare da yi wa jaruman addu’a Allah ya jikan wadanda suka rasu.

Ya samu rakiyar kwamandan, Brigade na Nijeriya, Birgediya-Janar. Isiyaka Olatunji da Group Captain Daniel Musa da Commander, 207 Kuick Response Group da Nigerian Air Force da Commissioner of Police Zamfara, Mista Ayuba Elkanah, da sauransu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *