Gasar cin kofin Ramat : An sanya sabuwar ranar farawa

Daga Ado Salisu
Hadaddinar kungiyar matasa magoya bayan wasanni ta kasa wato, Youths Sports Federation of Nigeria (YSFON) ta tsayar da sabuwar ranar da za a fara gasar cin Kofin tunawa da marigayi Janaral Murtala Ramat Muhammed, wanda aka fi sani da (Ramat Cup) ta wannan shekara da aka shirya za a gudanar a Kano.
Sakataren shirya gasar na Kasa, Abdulrazaq Usman ya fada a ranar Asabar cewa gasar wadda da za a fara gudanar da ita daga ranar 6 – 13 na Fabrairun wannan shekarar yanzu za a yi ta ne daga 19 ga watan Maris zuwa 23 kamar yadda kungiyar ta amince da sabuwar ranar.
Usman ya ce dukkan jihohi 36 na tarayyar da Babban Birnin Tarayya ana sa ran za su yi halarci gasar, domin fafutukar ganin jihar da za ta daga kofin.
A cewarsa, shugaban kungiyar na kasa, Dokta Nasiru Yusuf Gawuna wanda kuma shi ne Mataimakin Gwamnan jihar Kano ya bayar duk wasu kayan aiki da suka dace don samun nasarar gasar.
Gasar wacce aka dage ta tun da farko sakamakon karuwar cutar Korona, a yanzu an yarda da a fara ta bayan bin shawarwarin masu ruwa- da- tsaki da kuma yarda da bin ka’idojin da aka gindaya na kariya daga cutar Korona ga duk kungiyar da za ta fafata a gasar.
Ya ce Mataimakin Gwamnan da sauran mambobin kungiyar suna matukar yabawa gwamnan jihar Kano Dokta Abullahi Umar Ganduje saboda kokarinsa da jajircewarsa wajen taimaka wa kungiyar ta ci gaba da tunawa da marigayi Janar Murtala Ramat Mohammed wanda aka haife shi a jihar na jihar wanda kuma aka kashe shi a ranar 13 ga Fabrairu na shekar 1976.
Gasar ta ‘yan kasa da shekaru 16, na daya daga cikin kokarin kungiyar ta YSFON na ganin an bunkasa ci gaban matasa ta hanyar wasanni a kasar.