Gaskiyar magana kan Gwamna Badaru

Tura wannan Sakon


Daga: Habibu Nuhu Kila


Da wahala a bayyana yadda aka kai ga bayyana matakin da aka bi wajen samun sunan “Baba Mai Raskwana” (Calculator) ga wanda bai san gwamnan ba daga nesa, sai dai waxanda suka san shi kafin ya zama gwamna.
Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar ya jawo wa kansa xaukaka da bajinta da nagarta wajen hidimta wa jama’a cikin aikin gwamnati da tsarin da ba na gwamnati ba.
Badaru ya kasance xan-kasuwa na qasa da qasa a can lokaci mai tsawo kafin ya tsunduma kansa cikin harkokin saiya. Kaifin basira da nasarorinsa su suka haifa masa wajen qarfafa masa gwiwa daga ‘yan uwa da abokai kan ya zama xan siyasa.
Tunaninsu shi ne zai iya bayar da himmatuwa wajen kyautata tsarin arziqin jihar Jigawa tamkar yadda ake ganin zai iya yi fiye da haka idan ya zama shugaban tarayyar Nijeriya.
Bisa ga dukkan alamu, har zuwa yau xin nan, gwamnan bai kunyata waxanda suka ce, sun ji sun gani da halayyarsa ta shiga siyasa ba. Dalili, tun da ya zama gwamnan jihar Jigawa, jigawa ta tashi daga jerin jihohi masu fama da talauci zuwa jiha mai fama da ximbin albarkatu da raya kasa.
Ayyukansa nagari su suka haifar samar da ilimi ga talakawa da ‘yan qasa nagari masu dattaku waxanda suke zaune lafiya da juna cikin sanin haqqin Ubangiji SWT.
An rantsar da gwamnan ranar 29 ga watan Mayu, 2015 a wa’adisa na farko, inda ya fuskanci qalubale a karo na farko tamkar xaukar dala ne babu gammo, sai dai da shirya daga Ubangiji, kwakwaletar gwamna Badaru ta haskaka hanyar qarqashin qasa kuma hakan ya bai wa talakawa fata nagari lamari.
Basussukan da ya gada na kwangiloli na manyan ayyukan raya qasa, ya xara yawan kuxin kasafin kuxin jihar a shekara, watau kimanin Naira biliyan 110, a yayin da abin da ya iske a lalitar gwamnati Naira miliyan 16 kacal.
Mafi muni cikin lamarin, shi ne kuxin kason da Jigawa ke samu daga asusun gwamnatin tarayya wata-wata, ya sauka daga Naira biliyan 5 zuwa Naira biliyan 3, duk da haka gwamna bai razana ba. A qoqarinsa na fuskantar kalubalen tattalin arziqin jiha a lokacin, sai ya vullo da tsare-tsare da dabaru domin ya cim ma buri da buqatun mutanen jihar masu zave waxanda fatansu kawai su sharvi romon dimukuraxiyya kowa ya gani a qofar xakinsa.
A saboda haka, gwamnan ya rungumi qudurorin shugabanci nagari ta hanyar tabbatar da qididdiga da bayyana gaskiya qarara da sanin kimar kuxi.
A nan reskwana take aikinta, kuxaxen ba sa fitgowa daga lalitar gwamnati, sai an tantance gaskiya. babban xan kasuwa a cikin rigar gwamna, warware zare da abawa ga masu tunanin cewa, za a yi facaka da dukiyar talakawa.
Sha’anin shugabanci nagari ya sami gindin zama daram, domin kuwa an sake nazarin kuxaxen kashewa, da ake bai wa ma’aikatu da hukumomin gwamnati, an rage na ragewa, an qara na qarawa daga tsarin da aka gada.
A sakamakon haka, gwamna ya sami rarar kuxi wuri na gugar wuri har Naira biliyan 8 da digo 28 daga bisani aka yi amfani da su wajen kammala ayyukan raya qasa da ya gada tare da aiwatar da sababbi. Domin a cewarsa, almubazzaranci ne a yi watsi da ayyukan da aka ware biliyoyin Naira daga harajin da talakawa ke biya, ba a qarasa ba.
Kammala samun bayanin shekarar kuxi ta hannun ma’aikatar kuxi abin sai sambarka, domin kuwa an samu ci gaba wajen aiwatar da tsarin shekarar kuxi gwargwadon yawan kuxin kason da gwamnatin tarayya ke bai wa jihar.
Ma’aikatan gwamnati da takwarorinsu waxanda suka ajiye aiki, suna samun haqqoqinsu na wata-wata a kan kari, a sakamakon haka, sai da Jigawa ta karvi baquncin jihohi 20 da na tarayyar Nijeriya waxanda suka zo koyon dabarun da gwamnatin Badaru ta runguma.
A jihar Jigawa akwai tsarin raya qasa mai taken “kowane garin dagaci zai sami aiki xaya, al’amari ne na cin gajiyar gwamnati baixaya” Hakan ya haifa wa jihar kasancewa mafi kula da sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na hidimta wa jama’a babu voye-voye a duk faxin tarayyar qasar nan.
Jihar ita ce a sahun gaba wajen gina nagartattun hanayoyin mota masu tsawon kimomita 1,600 domin sauqaqa sha’anin sufuri. Kowane garin dagaci an gina masa cibiyar kiwon lafiya domin kula da kiwon lafiyar jama’a duk a qarqashin gwamnatin Badaru.
Jigawa ta yi wa takwarorinta fintinkau wajen samar da ruwan famfo, ga jama’a a fadin kasar nan, domin a qarqashin gwamna Badaru kowane bangare ya sami kulawa sosai. Gwamnati ta kuma bai wa vangaren kashe kuxin gwamnati kima wajen aiwatar da shirye-shirye da ayyukan raya qasa.
Kwamared Badaru na jihar Jigawa ya yi wa takwrorinsa fintinkau wajen sama wa ma’aikata da qungiyoyinsu a Nijeriya inda har ta kai qungiyar ma’aikatan qananan hukumomin (NULGE) ta karrama shi da lambar yabo mafi xaukaka. Shugabanci nagari da ya haifa wa Badaru kasancewa xan kasa mai xa’a domin kuwa shugabanci nagari ya taimaka ainun wajen qarfafa sha’anin dimukraxiyya, da tsarin tattalin arziqi da haxa kan jama’a da rage raxaxin fatara da amfani da alabarktun qasa da amincewa da gwamnati a zukatan jama’a.
A saboda haka, Badaru shi ya fi cancanta ya zama shugaban Nijeriya wanda zai gaji shuba Buhari.
An haifi Muhmamdu Badaru Abubakar MON mni a ranar 29 ga Satumba 1062 a garin Babura cibiyar mulkin qaramar hukumar Babura a jihar Jigawa.
An sanya shi a makarantar firamare ta Vavura a shekara ta 1970, bayan kammala ta ya zarce zuwa fitacciyar kwalejin Rumfa da ke birnin Kano, inda ya kammala a shekra ta 1981, ya kuma sami takardar shaidar ilimin sakandare.
Daga nan ya zarce zuwa jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, domin zurfafa iliminsa, inda ya kammala a shekera ta 1985 ya kuma samu takardar shaidar ilimi ta digiri a kan fannin lissafi ko sha’anin kuxi.
Ya kuma yi aiki da sashin binciken kuxi na jihar Kano, wanda ke qarqashin ma’aikatar kuxi ta jihar.
Muhamadu Badaru ya kafa kamfaninsa mai sua Talamiz domin gudanar da harkokin kasuwanci, bayan ‘yan shekaru sai kamfanin ya bunqasa ya zama Talamiz Nigeria Limited. Kamfanin ya sami nasarar samar da rassa da yawa a qarqashinsa a dunqule waje xaya, waxanda suka haxa da shigo da motoci daga qetare da samar da kayayyaki na masana’antu da ayyukan noma da kiwon dabbobi da rarraba kayayyakin masarufi.
A shekara ta 2006 Muhammadu Badaru ya je qaro ilimi a cibiyar nazarin muhimman buqatu da dabaru da tsare-tsaren qasa, da ke Kuru kusa da Jos, jihar Filato.
A matsayinsa na hamshaqin xan kasuwa na qasa da qasa, bayan kammala karatunsa, Muhamamdu Badaru ya kafa rukunonin kamfanonin Talamiz masu tafiyar da harkokin kasuwanci nau’i-nau’i, kamar shigo da manyan motoci da samar da kayayyakin masana’antu, da ayyukan noma da kiwon dabbobi da kuma rarraba kayayyakin masarufi, daga bisani Badaru ya zama shugaban dukkanin kamfanonin da aka ambata a baya.
Yana riqe da laqabin sarautun gargajiya da ya samu, waxanda suka haxa da Walin Jahun, a jihar Jigawa, da Sardaunan Ringim a masarautar Ringim da Dokajin Machina a jihar Yobe.
Har ila yau, shi ne shugaban cibiyar kula da masana’antu da kasuwanci da noma ta jihar Jigawa, shugaban cibiya irinta wadda ta haxa Nijeriya da Nijar, shugabanta na jihohin Arewa 19, shugaban hukumar amintattu ta jihohin Arewa kuma shugaba na qasa na qungiyar masu motocin sufuri ta Nijeriya, reshen jihar Jigawa.
Badaru Abubakar mamba ne na qungiyoyin jama’a da cibiyoyin kwamitin bayar da shawara kan masana’antu na ofishin shugaban qasa, da cibiyar masana’antu da kasuwanci tsakanin Amirka da Nijeriya, da cibiyar yi wa masana’antu da kamfanoni rijista, mamba ne a cibiyar masana’antu tsakanin Nijeriya da Belgium, da cibiyar cefanar da kamfanonin gwamnati kuma ya halarci babban taron fasalta Nijeriya a shekara ta 2014.
Ya tava zama darakta a bankin Africa Merchant, da Bankin Arewa (Bank of the North) Unity Bank kenan yanzu, Uban qungiyar masu noman shinkafa da qungiyar ‘yan jaridun Nijeriya (NUJ).
Baya ga kasancewarsa xan cibiyar nazarin muhimman baqatun qasa (mni) Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar Uba ne ga qungiyar akantoci ta Nijeriya FCNA kuma ya sami lambar girmamawa ta qasa mai laqabin MON da aka ba shi a shekara ta 2006 kuma ya halarci kwasa-kwasai da dama, gida da waje.
Alhaji Muhammadu Badaru Abuabakr xan majalisar cefanar da kadarorin qasa ne ta tarayyar Nijeriya. Ya kasance mataimakin shugaba na biyu a cibiyar kasuwanci ta yammacin Afirka (REWACCI).
Ya fara aikin gwamnati a matsayin mai binciken kuxi a qarqashin ma’aikatar kuxi ta jihar Kano daga shekarar 1987 zuwa 1991, inda ya bar aiki kuma ya kafa kamfaninsa na Talamiz.
Daga bisani kamfanin ya haifar da kamfanonin da suka haxa da Talamiz Motors, Talamiz Consumer Company, Talamiz Transport, Talamiz Commodities, Oil Mill Limited, Socar Talamiz Limited, RMR Shipping BV, ALM Bonded Talamiz, ALUAFRIC Cairo kuma darakta na Salih Nijeriya Limited.
A shekara ta 2011, Badaru ya yi takarar gwamna tare da sule Lamixo amma bai sami nasara ba.
A watan Afrilu 2015, Badaru yayi takarar muqamin gwamna a jihar a qarqashin jam’iyyar APC kuma ya sami nasara kuma aka rantsar da shi a ranar 29 ga May, 2015.
Gwamna Badaru shi ne shugaban kwamitin ofishin shugaban qasa kan harkar rabon taki kuma shugaban kwamitin samar da kuxin shiga ba ta hanyar albarkatun man fetur ba.
Ya kuma shugabanci kwamitin gudanar da babban taron APC na qasa kuma shugaban kwamitin gudanar da zave, baya ga waxansu kwamitoci na zavukan share fage a jihohi daban-daban, bugu da qari ya shugabanci kwamitin gwamnonin da suka sauya sheqa zuwa APC.

Habibu Nuhu Kila
Babban mashawarci na musamman ga gwamna
Kan harkokin yaxa labarai da hulxa da jama’a
Ga gwamnan jihar Jigawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *