Gawuna, akili da sanin yakamata -In ji Usman

Za mu bude madatsar Tiga cikin Yuni –Gawuna

Alhaji Nasiru Yusif Gawuna,

Tura wannan Sakon

An bayyana dan takarar gwamnan jihar Kano a karkashin jam’iyyar APC, Dokta Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin akilin mutum mai sanin ya kamata

. Jawabin haka ya fito daga bakin Nuraddeen Muhammad Usman a lokacin da yake ganawa da manema labarai ciki harda wakilin jaridar Albishir a Kano. Ya ce, Gawuna akilin mutum shi ne wanda ba ya yi wa gaskiya girman kai.

Alhaji Nuraddeen Muhammad Usman shi ne shugaban kamfanin AU Gama Inbestment ya ce, Dokta Nasiru Yusuf Gawuna akili kuma cikakken mutum mai son zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaban al’umma, uwa uba shi kadai ne dan siyasa da yake fita ba tare da ‘yan jagaliya ba kuma shi ne wanda makiyansa ma kaunarsa suke domin ba shi da abokin gaba.

Ya kara da cewa, jam’iyyar NNPP yaudara ce kawai domin ba ta da munufa kuma lokaci ya yi da za a daina yaudarar mutane musamman matasa. Ya bayyana cewa, a Kano ne ake siyasar neman kujera ba siyasar ci gaban jama’a ba, domin za ka ga dan siyasa ya fito daga wata jam’iyya ya koma wata domin neman takarar kujera kawai.

Daga karshe, ya yi kira ga matasa su zabi cancanta ba alaka ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *