Gawuna, ya cancanci zama gwamna -Musa Maitakobi

Muhammad Kano
An bayyana mataimakin gwamnan jihar Kano kuma dan takarar gwamnan jihar a jam’iyyar APC, Dokta Nasir Yusuf Gawuna da cewa, yana da nagarta da kwarewa a kan sanin makamar mulki da iya kyakkyawar mu’amala ta girmama jama’a, da ya dace da zama gwamna.
Shugaban Kungiyar RTEAN na kasa Alhaji Dokta Musa Muhammad Maitakobi ne ya bayyana hakan da yake zantawa da ‘yan jarida. Ya ce, irin wannan nagartar ta Gawuna ta sanya suka ba shi goyon baya da nuna manufofinsa ga al’umma, domin ya kai ga nasara a zabe na 2023.
Ya kara da cewa, Gawuna, ta fuskar gudanar da ayyukan gwamnati ya san wadanda aka yi da wadanda aka fara ba a karasa ba, wanda idan aka zabe shi zai karasa ya kuma dora da wanda zai yi.
Maitakobi ya jaddada cewa, wannan na daga abin da ya ja ra’ayinsa ya ga dacewar a matsayinsa na dan asalin jihar Kano, ya bayar da tasa gudummuwar ta hanyar da Gawuna zai sami mulkin Kano cikin ikon Allah, kuma zai sami nasara.
Ya yi nuni da cewa, nagartar mutum ita ce sanin darajar mutane,da sanin yadda zai taimaka musu da tafiya da su, wanda a cewarsa duka dabi’un Gawuna ne, don haka ya ga ya kamata ya bayar da gudummuwa domin ganin ya kai ga yin nasara, domin zai amfani al’ummar Kano.
Alhaji Dokta Musa Muhammad Maitakobi ya yi nuni da cewa, abin da ake kula ga kowane dan takara shi ne, yaya yake da jama’a wajen tafiya da su, ya yake tafiyar da mu’amala a aikinsa da kuma a unguwarsa da wadanda yake tare da su da jama’a na waje da ba unguwarsu ko wajen aikinsu daya ba.
Ya kara da cewa, Gawuna mutum ne da ya sami yabo a wajen jama’a, kuma yana da mutukar wahala ko wadanda ba sa jam’iyya daya da shi idan an tambaye su suna cewa, mutum ne mai nagarta da sanin yakamata.
Maitakobi, wanda asalin iyayensa sun fito daga yankin Gezawa, a jihar Kano ne, amma haifaffen jihar Yobe ne, ya yi nuni da cewa, duk wanda yake danganta halin da kasar nan take ciki da cewa mulkin APC ne ya jawo, ya yi kuskure, idan Musulmi ne ya sami dimuwa, domin Allah ba ya canza mana wani abu na rayuwa sai mun canza wa kanmu, a cewarsa.
Ya ce, duk wanda ya ce dalilin wannan jam’iyya da ke mulki shi ya sa aka shiga matsala, wannan kuskure ne, domin Allah ya ce, duk wanda ya ji tsoronsa ga irin sakamakon da zai masa, inda ya kara da cewa, ya kamata mutum ya san me yake yi.
Bayan haka, Allah ya ce, duk wanda ya ji tsoronsa zai sa al’amuransa su zama masu sauki a gare shi. Ya kuma ce, “abin da ya kamata a duba a yi bincike a ji tsoron Allah, mun kaucewa bin Allah ne, sai ya jarrabe mu, domin idan fasadi ya yi yawa kada a ce Allah ba zai jarrabe mu ba, zai jarrabe mu” a cewarsa.
Maitakobi ya kuma shawarci al’ummar kasar nan da su sani cewa, zabin Allah shi ne zabi ba zabin mutane ba, don haka a duk inda suke su yi addu’ar Allah ya zaba mana shugabanni nagari, domin za ka iya zabar wanda kake so, idan bai zama zabin Allah ba, ba zai zama na kirki ba, amma idan muka tattara dukkan al’amurammu muka mika ga Allah zai mana zabi na alkhairi.