Gidauniyar Masari ta yi wa Mutane 500 Aikin Ido

Tura wannan Sakon

Daga Muawuya Bala Idris, Katsina

Wata qungiya, wacce ba ta gwamnati ba, Gidauniyar Aminu Bello Masari ta qaddamar da gyaran idanu ga mutane 500.

Gyaran idon wanda aka qaddamar a asibitin ido da ke tsohuwa kasuwa zai xauki tsawon kwana uku ana gudanarwa.

Wakilinmu wanda ya halarci qaddamarwa ya rawaito cewa, mutane daga garin Katsina da Jigawa da Niger Republic sun yi dafifi domin amfana da taimakon.

Da yake magana da manema labarai, shugaban Gidauniyar, Kabir Abdullahi Mashi ya ce, gyaran idanun kyauta ne don taimakawa masu karamin karfi da suke dauke da wannan lalura.

 Mashi ya ce, Gidauniyar ta lura cewa, da yawa daga cikin masu lalurar ba su da kuxin xaukar nauyi magani.

Ya ci gaba da cewa, cikin adadin waxanda za su amfana, akwai waxanda za’a ba su gilashi da magunguna waxansu kuma za’a yi ma su tiyata Mashi wanda shi ne Kaigaman Katsina ya ce, za a faxaxa aikin ga duk faxin jihar.

Tun farko, shugana asibitin idanu na Katisna, Dokto Ahmed Hamza ya ce, jihar tana da masu matsalar yanar idanu har mutane dubu 30. Hamza ya ce, Gidauniya ta yi namijin qoqari domin tuni ta samar da magunguna da duk abin da ake buqata domin yin aikin.

 Ya roqi Gidauniyar ta taimaka wajen samar da ruwan famfo da magance matsalar wutar lantariki a asibitin. Hamza ya yi kira ga sauran qungiyoyi da masu hali da su xauki nauyin yin aiki ga mutane masu lalura yanar idanu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *