Gobe ranar rage kiba ta Duniya: A karo na farko, asibitin Aminu Kano ya yi tiyatar rage kibar

Tura wannan Sakon

Fassarar Aliyu Umar

Asibitin koyarwa na Aminu Kano da ke Kano ya sami nasarar yi wa dan shekaru 60 da haihuwa tiyatar rage kiba.

Kwararrun likitocin tuntuba a asibitin bisa jagorancin,Dr. Bello Usman,ya ce,wanda aka yi wa tiyatar yana da nauyin kilogiram 156.

Takardar bayani da ke dauke da sanya hannun mataimakiyar daraktar yada labarai da hulda da jama’a ta asibitin,Hajiya Hauwa Muhd Abdullahi, ta ce,an zartar da yi tiyatar rage kibar ne domin ya yi daidai da bikin ranar rage kiba ta Duniya,a karkashin Majalisar dinkin Duniya.

Tun da farko dai,wanda aka yi wa tiyatar,shi ya kawo kansa asibitin kan yana fama da cututtukan da suka hada da hawan jini da suga da kuma zuciya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *