Gumi ya kafa kungiyar kare Fulani makiyaya

Tura wannan Sakon

Shaharren malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya kafa kungiyar da za ta kare Fulani makiyaya.

Gumi ya sanar da kafa kungiyar da ya kira kungiyar kare hakkokin Fulani makiyaya, watau NORIC (Nomadic Rights Concern) a yayin gudanar da tafsirin watan Ramadan a masallacin sarkin Musulmi Bello, Kaduna.

Ya ce, kungiyar za ta janyo hankalin al’umma a game da cin zarafin da ake yi wa Fulani makiyaya.

Ya bayyana Farfesa Umar Labbo a matsayin wanda zai jagoranci kungiyar, yana mai cewa, NORIC za ta zama wata kafa da makiyaya za su kai korafe korafensu game da abubuwan da ke ci masu tuwo a kwarya zuwa ga hukumomin da suka dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back To Top