Gwamna Ganduje, shugaba adali-In ji Hayin Hago

Tura wannan Sakon

Daga Jabiru Hassan

Wani jigo a jam’iyyar APC daga mazabar Dawaki Ta Gabas, Karamar hukumar Dawakin Tofa Alhaji Sa’ad Muktar Hayin Hago yace gwamnan jihar kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje shugaba ne mai adalci wanda kuma yake da hangen nesa saboda kwarewar sa a siyasa.

Yayi wannan tsokaci ne a hirar su da wakilin mu, inda kuma ya nunar da cewa ko shakk babu, gwamna Ganduje shugaba ne nagari kuma mai matukar kishin jihar kano wanda a cewar sa, hakan ta sanya jihar kano ke samun ci gaba mai kyau a tsari irin na dimokuradiyya. Alhaji Sa’ad Hayin Hago ya kara da cewa.

“ mun gamsu da yadda maigirma gwamna yake jagorantar jihar mu domin kuwa daga shekara ta 2015 zuwa yau, an cimma nasarori masu tarin yawa a jihar kano kuma an gudanar da aikace-aikace masu aminci kuma ana yin wasu wadanda zasu amfani al’uma har ma ‘ya’ya da jikoki masu zuwa nan gaba”.

Bugu da kari, dan siyasar ya sanar da cewa ana samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar ta kano sakamakon kokari da gwamnatin Ganduje keyi na assasa addu’oi a masallatai da sauran guraren taruwar al’uma da kuma daukar matakai da gwamnati keyi wajen tabbatar da cewa ana zaune lafiya kamar yadda ake gani a yau.

Sannan yayi waiwaye kan yadda gwamnati ke daukar kwararan matakai kan cutar Korona domin ganin wannan annoba bata yadu cikin al’uma ba wanda hakan ta sanya al’umar jihar kano suke kallon gwamnatin ta Gaduje a matsayin gwamnati ai kula da lafiyar su batare da nuna gajiyawa ba.

A karshe, Alhaji Sa’ad Muktar Hayin Hago ya yabawa al’umar jihar kano saboda fitowa da suke yi wajen sabunta katin su na zama dan jam’iyya wanda hakan ya tabbatar da cewa mutanen jihar kano APC suke yi kuma ita suke goyon baya saboda kyautata rayuwar su da gwamnatin Ganduje keyi a birni da yankunan karkara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *