Gwamna Yobe ya gina hanyoyi a babban birnin jihar

Tura wannan Sakon

Yusuf M. Tata Damaturu

A shirin samar da sauqin zirga-zirga a cikin garin Damaturu da ke[1]waye, gwamnatin Mai Mala Buni ta gina hanyoyi da ma[1]gudanan ruwa da tsawon su ya kai kilomita 17.

Kwamishinan ayyuka na jihar, Injiniya Umar Wakili ya bayyana wa manema labarai haka a Damaturu inda wurar[1]en da suka ci gajiyar hanyoyin da magudanun ruwa. Ya ce, dukkan hanyoyin da magudanan ruwa an kam[1]mala su kuma ana sa ran za su kawo sauqin zirga-zirga a jama’ar da suke wuraren da aka yi wadannan hanyoyin.

Kwamishinan ya ce, ak[1]wai wadansu hanyoyi da har yanzu ana kan aikin gina su watau hanyar Damagum zuwa Gubana da hanyar Garin Bin[1]gel zuwa Danchuwa sauran su ne hanyar Nguru zuwa Bal[1]anguwa sai Balanguwa zuwa Kumaganam Chumbusko zuwa Tagali.

Ya qara da cewa, tuni gwamnatin jihar a qarqashin gwamnan Mai Mala Buni ta kammala ginin hanyar sama a kasuwar shanu da kuma ka[1]suwar zamani da ke Damatu[1]ru, ana sa ran gina hanyoyin sama a sababbin kasuwannin zamani na Nguru da Gashua da Potiskum.

Daga qarshe, ya ce ba sa yin qasa a gwiwa wajen kai wa agajin gaugawa inda ta gaggauta samar da mafita a garin Katarko da ke qara[1]mar hukumar Gujba lokacin da ruwa ya karya gada ya kawo tsaiko wajen zirga-zirga tsakanin Damaturu da Gujba harzuwa qasar Biu da ke jihar Borno

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *