Gwamnan Bauchi ga mahajjata: Ku kasance jakadu na kwarai

Idan masalaha ta gagara, ba na tsoron bugawa da kowa -Bala Mohammed

Bala Mohammed

Tura wannan Sakon

Jamilu Barau Daga Bauchi

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Muhammed ya jaddada kudirin gwamnatinsa na samar wa ‘yan kasa ribar dimukuradiyya, ya kara da cewa, samar da zaman lafiya da hadin kai a jihar shi ne babban abin da ya fi fifitawa.

Bala Muhammed ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da maniyyatan jihar da jami’an hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Bauchi a Sabon sansanin Alhazai na jihar, inda ya yi kira gare su da su kasance jakadu nagari a Nijeriya kafin tafiyarsu da kuma bayan an kammala aikin Hajji.

Bala Muhammed ya kara da yaba wa hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON), da malamai da masu ruwa da tsaki cikin masu kula da jigilar mahajjata, ya ce, gwamnatin jihar za ta hada kai da su domin ganin an samu nasarar aikin Hajjin na 2022.

Ya kara da yin kira ga maniyyatan jihar Bauchin wanda yawansu ya kai 1363 da su yi wa jihar Bauchi da Nijeriya addu’a, ya kara da cewa, an yi duk wani shiri na ciki da waje domin saukaka masu wahalhalu da za su fuskanta a yayin aAikin Hajjin na bana.

Da yake mayar da martani, Amirul Hajji na jihar kuma Sarkin Katagum, Alhaji Umar Farouk ya yabawa gwamna Bala bisa gina sansanin Hajji na zamani tare da ba shi tabbacin goyon bayansu domin samun nasarar aikin.

A sauran masu jawabi da suka biyo baya, uwargidan gwamnan jihar, Hajiya A’isha Bala Muhammed da sakataren zartaswa ta hukumar jin dadin Alhazai, Imam Abdurrahmam Ibrahim Idris sun yaba wa gwamna bisa kokarinsa na ganin an samu sauki ga ‘yan kasa tare da yin kira ga maniyyatan da su mayar da hankali wajen yi wa gwàmnan addu’an alheri da samun nasara ga gwamnatinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *