Gwamnan Bauchi ya gwangwaje hukumar kashe gobara da motoci

Gwamnan Bauchi ya gwangwaje hukumar kashe gobara da motoci

Gwamnan Bauchi ya gwangwaje hukumar kashe gobara da motoci

Tura wannan Sakon

Jamilu Barau Daga Bauchi

Gwamnatin jihar Bauchi karkashin gwamna Bala Abdulkadir Muhammed, Kauran Bauchi ta bayar da gudunmawar motocin kashe gobara a kokarin gwamnatin jihar na dakile tsaiko da ake samu kan kai agajin gaggawa duk lokaci da bala’in, gobara ta afku a jihar.

Sakataren gwamnatin jihar, Barista Ibrahim Kashim ne ya gabatar da makullan motocin da aka bayar, ga hukumar sannan ya yi kira gare su su yi kokarin rike motocin amana yadda za a jima ana cin moriyarsu.

Ya ce, bayar da motocin kashe gobara na daga cikin kudirin gwamnatin gwamna Bala Muhammed na samarwa hukumar kashe gobara kayan aiki masu inganci domin sauke nauGwamnan Bauchi ya gwangwaje hukumar kashe gobara da motoci yin da ya rataya a wuyan gwamnati.

Sakataren gwamnatin ya ce, gwamna Bala Muhammed, ya siyomotocin ne ga hukumar kashe gobara domin inganta ayyukasu, muna sane da cewa, hukumar kashe gobara a jiharmu na fuskantar kalubale dangane da rashin kayan aiki na zamani da motocin da muke bayarwa a yau.

Barista Kashim ya yi amfani da wannan damar wajen tabbatar wa al’ummar jihar cewa, gwamnatin jihar na yin duk mai yiwuwa wajen samar da motocin kashe gobara na zamani a kowace karamar hukumar jihar domin rage masu wahalhalu da suke fuskanta lokacin bala’in gobara.

Da yake jawabi, daraktan hukumar kashe gobara na jihar Bauchi, Injiniya Bala Garba ya nuna jin dadinsa ga gwamna Bala bisa tallafin motocin, inda ya bayar da tabbacin yin amfani da su yadda ya kamata ta hanyar tunkarar bala’in gobara cikin gaggawa a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *