Gwamnan Bauchi ya yi tir da cire al’aurar yarinya

Tura wannan Sakon

Jamilu Barau daga Bauchi

Gwamna Bala Muhammad Abdulkadir na jihar Bauchi ya yi Allah wadai da cire wani fannin al’aurar wata yarinya yar’ shekara shida a karamar Hukumar Jama’are da ke jihar Bauchi.

Kwamishinan kananan hukumomi da masarautun gargajiya, Alhaji Abdulrazak Nuhu Zaki ne ya bayyana hakan a lokacin da ya jagoranci kwamiti mai karfi wadda suka kai ziyarar duba yarinyar da iyayen ta kan abinda ya faru a Jama’are.

Kwamishinan ya bayyana irin wannan abu a matsayin rashin imani kuma abu ne wadda ba za su taba yadda da shi. Alhaji Nuhu Zaki ya kuma yi alkawarin cewa, gwamnatin jihar Bauchi za ta yi dukkan mai yiyuwa domin ganin an yi adalci ga wannan yarinyar an kuma bayar da tallafin kayan abinci da kudi’ wa iyalan yarinyar .

Maigirma gwamna Bala Muhammad Abdulkadir wannan alamari ya taba duciyarsa matuka a madadin shi kansa na jajanta wa yan’uwa da iyayen wannan yarinyar na wannan abu da ya faru, ya ce, gwamnati kuma za ta yi dukkan mai yiyuwa na daukar nauyin jinyar yarinyar duka har ta samu lafiya.

Gwamnati za ta dauki duka dawainiyarta har ta samu lafiya saboda gwamna na son ganin ya ga al’ummarsa na cikin walwala musamman marasa karfi. Ya kara da cewa, gwamnati za ta dauki mataki mai karfi kan wadanda suka aikata wannan al’amari domin ya zama izina ga matasan da suke da irin tunani, domin asamu tsaftaceccen al’umma.

Kwamishinan mata da jindadin yara, Hajiya Hajara Gidado ta isar da sakon Uwargidan gwamna, Hajiya Aisha Bala Muhammad a lokacin ziyarar, ta ce Uwargidan gwamna yanzu haka ta bayar da umurinin yin wani kwamiti mai karfi wadda ya kunshi masana shari’a da lauyoyi kan wannan iftili’i da rashin tausayi da aka yi wa yarinyar don sufuskanci shari’a.

A nasa jawabin, Kwamishinan lafiya, Dokta Aliyu Maigoro ya ce abin da a yandu yarinyar ke bukata shine amata aiki ‘’Plastic Surgery” domin samu ta farfado ta yi rayuwarta a matakin farko.

Iyalan yarinyar sun bayyana godiyarsu wa gwamnatin Bala Muhammad Abdulkadir na nuna kulawa da damuwa da shigowa cikin wannan al’amari da ya faru da su cikin gaggawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *