Gwamnan Gombe Ya Nada Sabon Mai na Tangle

Tura wannan Sakon

Daga Mahmud Gambo Sani

A bisa ikon da aka ba shi a ƙarƙashin dokar sarauta ta jihar Gombe, ta shekarar 2020, da kuma shawarar da sarakunan Tangale suka bayar, Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya ya amince da nadin Malam Danladi Sanusi Maiyamba a matsayin sabon Mai na Tangle.

Kwamishinan Ma’aikatar kananan hukumomi da al’amuran masarauta na jihar, Ibrahim Dasuki Jalo wanda ya isar da takardar amincewar Gwamnan ga sabon Mai na Tangle a karamar hukumar Billiri, ya ce nadin Malam Danladi Maiyamba ya tabbata ne a bisa laakari da kyawawan halayensa da cancantarsa.

Bikin gabatarwar da takardar nadin ya samu halartar shugabar karamar hukumar Billiri da masu nada sarki su tara na masarautar da kuma sauran mambobin majalisar sarakunan gargajiya da sauran al’umma.

A nan gaba za a Gabatar da bikin nadin sarautar da bayar da sandar mulki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *