Gwamnati, a gyara hanyoyin Nijeriya -Badamasi

Generated by IJG JPEG Library
Daga Wakilinmu
An yi kira ga gwamnatin kasar nan a qarqashin shugaba Muhammadu Buhari, da ta qara qaimi wajen gyara manya da qananan hanyoyin qasar nan, ganin yadda lalacewar ke jawo rasa rayukan matafiya da dukoyoyinsu.
Bayanin haka ya fito ne daga bakin shugaban qungiyar motoci na N U R T W na tashar Dorayi Babba dake jihar Kano, Kwamared Badamasi Idris Murtala, a lokacin da yake zanatawa da manema labarai a Kano, ciki har da jaridar Albishir.
Kwamared Badamasi Idris Murtala, ya qara da cewa, kusan kullum sai an samu asarar rayuka da dukiyoyin al’umma, sakamakon lalacewar hanyoyin, matuqar gwamnatin ta gyara hanyoyin zai kawo qarancin rasa rayuka da dukiyoyin da ake yi da yardar Allah inji City Boy.
Shugaban tashar ya kuma shawarci gwamnatin ta taimaka wa direbobin da ke cikin qungiyar, musamman matasa da motoci da za su riqa biya a hankali har su kammala biya, soboda akwai matasa masu dinbin yawa da basu da motar da suke aiki da ita duk da kasancewa suna da basiran iya tuqin mota .
Amma a matsayin shima shugaban qungiya yana bakin qoqarinsa, wajen ganin wadansu daga cikin matasan sun samu mota, inda ya zuwa yanzu ya taimaka wa da wadansu daga ciki motocin da suke aiki da su maimakon su zauna babu aikin yi.
Alhaji Badamasi wanda har ila yau shi ne mataimakin tsare-tsare na qungiyar ta NURTW na jihar Kano, ya yi kira ga ‘yan qungiyar da ke fadin jihar, da su ci gaba da bai wa qungiyar hadin kai da goyon baya domin qungiyar da kai ga nasarorin da ake buqata, sannan su kasance masu gaskiya da amana tare da sanya tsoron Allah a cikin harkokinsu na tuqin mota.
Daga qarshe, ya yi addu’ar Allah ya kawo mana qarshen matsalolin tsaro da qasar nan take fama da shi, musamman na garkuwar da ake yi a kan manyan hanyoyin qasar nan.