Gwamnati, a shiga tsakanin ‘yan-kasuwa da kwastan

Tura wannan Sakon

Daga Isma’il Usman Katsina

A zaman tattaunawa da muka yi da masu ruwa da tsaki a harkokin dabbobi an fahimci bukatun makiyaya samun filayen kiwo da mashaya ruwa da makarantun Islamiyya da masallatai da makarantun boko da asibitoci na mutane da na dabbobi da muhimmin al’amari da hanyoyi da wuraren da dabbobi suke bi domin kiwo ya fi kilo mita dubu 2.

Sannan kuma mun sa harsashin iyakoki gonakin ciyawa tare da gyara damdam da ke bukatar gyara domin tanadin isasshen ruwa, wanda za a iya amfani da shi domin noman rani ga mazauna wurin.

Dokta Lawal Usman Bagiwa ya bayar da tabbacin gyara tsofaffin makarantun rugage fiye 100 da muke da su a jihar nan domin bunkasa ilimi. Muna da niyyar yin wani abu muhimmi ga kowace karamar hukuma daga cikin goman nan da suka samu kawunansu cikin baraza ta tsaro.

Kuma duk damana za mu ba makiyayan hekta daya domin su noma , idan sun kai su dubu za ab bai wa kowace hekta daya aro ba kyauta ba, kuma za su samu tallafi na taki da iri wanda za su shuka.

Kamfanoni daban-daban har guda 17 suka amsa kiranmu tare da Romon gabatar da takardunsu na irin ayyukan da suke yi da kudin aikins , wadanda suke son su yi aiki da mu.

Bayan mun gama tantancewa mun zabi kamfanoni guda shida kowane zai yi zaman kansu kuma su yi aiki kala daban-daban, misali muna da kamfani wanda zai yi mana tsaretsaren yadda aikin zai kasance.

Akwai kamfanin da zai yi binciken yanayin kasa, muna da wanda zai zana ayyukan ya yi taswirar ayyukan baki daya, sai kuma wanda zai yi kiyasin kudin da kowane aikin za lakume.

Idan an gama sai ‘yan kwangila da za su yi aikace-aikacen gine-ginen. Mu kuma a Ma’aikatance za mu rinka bi tare da ma’aikatanmu wadanda suka kware a fannoninsu muna duba nagarta da dacewar aikin da ake yi, dukkan yunkurin da muke yi muna san daga watan biyu zuwa uku na wannan shekarar mun gama Insha Allah daga watan 6 zuwa 6 an kammala dukkan ayyukan mun kama aikinmu gadan-gadan a cewa mai bai wa gwamna shawara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *