Gwamnati, a taimaka wa manoma na gaskiya -In ji Mado

Buhari, shugaba mafi talauci a Afirka

Buhari, shugaba mafi talauci a Afirka

Tura wannan Sakon

Matukar gwamnatin kasar nan tana son ciyar da kasar nan da abinci, to babu shakka sai ta mayar da hankalin ta wajen taimaka wa tsantsan manoma na gaskiya, saboda yawancin taimakon da take bayar wa ba ya zuwa ga manoman da ake bukata.

Baynin haka ya fito ne daga bakin wani manomi dankasuwa da ke sana’ar sayar da kayan abinci a kasuwar Dawanau a Kano, Alhaji Muhammadu Usman da aka fi sani da Mado, a lokacin da yake zantawa da manema labarai a kasuwar. Muhammadu Usman ya kara da cewa, matukar gwamnatin ta taimaka wa manoman da ake bukata za su iya ciyar da kasar nan da abinci har a kai shi wadansu kasashe.

Idan kuma gwamnatin za ta bayar da tallafin noma ta rika bayar wa a kan lokaci musamman kafin faduwar damuna. Alhaji Muhammadu Usman ya sharwarci shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa, duk wanda ya bai wa mukami ya rinka sanya ido tare da bibiyar halin da ake ciki.

Game da matsalolin tsaron da kasar nan take fuskanta. Mado ya ce, babu abin da zai fitar da mu sai an koma ga Allah tare da addu’a idan aka yi haka da yardar Allah za’a fita, kuma al’umma suka kara bai wa gwamnati da jami’an tsaro hadin kai da goyon baya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *