Gwamnatin Ganduje ta ciri tuta wajen bunkasa ilimi -In ji Dokta Kabir Bello

Tura wannan Sakon

Labari Jabiru A Hassan, Daga Kano

Shugaban kwalejin fasaha ta jihar Kano, Dokta Kabir Ballo Dungurawa ya ce, ko shakka babu gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje ta cancanci yabo dangane da kokarin da take yi wajen bunkasa ilimi a matakai daban-daban.

Ya yi tsokaci ne a jawabin da ya gabatar ranar Talatar da ta gabata yayin bikin aza harsashin ginin wani katafaren dakin daukar karatu na zamani wanda zai dibi dalibai 160 da cibiyar kwararru kan aikin banki da hadahadar kudade watau “Chartered Institute Of Banking Of Nigeria” (CIBN) za ta gina a makarantar samun kwarewa kan sha’anin gudanarwa ta “ School Of Management Studies “.

Dokta Dungurawa ya kara da cewa, babu shakka muna masu matukar alfahari da irin goyon baya da kuma kulawa cikakkiya da gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje ke bai wa fannin ilimi a fadin jihar Kano, duk da irin kalubalen da ake ciki na yanayin tattalin arziki da kuma gudanar da harkar ta ilimi, domin haka wajibi ne mu jinjina wa gwamna da gwamnatin sa saboda kokari da ake yi”. In ji shi.

Dangane da yadda cibiyar CIBN take aiwatar da Gwamnatin Ganduje ta ciri tuta wajen bunkasa ilimi -In ji Dokta Kabir Bello ayyukanta kuwa, Dokta Kabir Bello Dungurawa ya jaddada farin cikinsa saboda samar da babban zauren daukar darussa irin na zamani da ta fara ginawa a makarantarsa, tare da bayyana cewa, da yardar Allah, za su yi amfani da gurin, domin bunkasa koyo da bincike kan dukkanin abubuwan da suka shafi ilimin aikin banki.

Dokta Dungurawa ya yi amfani da wannan dama inda ya gode wa maimartaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero da kwamishiniyar ma’aikatar ilimi mai zurfi, Hajiya Mariya Mahmoud Bunkure da shugabamnin jami’oi da kwalejojin ilimi da kuma dukkanin masu ruwa da tsaki kan harka ilimi saboda halartar bikin da suka yi duk da irin harkokin aiki yake gabansu.

Wakilin mu ya sami zantawa da shugaban kungiyar dalibai masu karatu a fannin aikin banki, Kwamred Nasiru Isah Musa inda ya shaida wa Albishir cewa, gwamna Ganduje ya cancanci yabo da godiya saboda kyautata fannin ilimi da yake yi ba tare da nuna kasala ba, sannna ya bayyana shugaban kwalejin fasaha ta jihar Kano, Dokta Kabid Bello Dungurawa a matsayin shugaba wanda ya kawo ci gaba ingantacce a makarantun da ke karkashin ikonsa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *