Gwamnatin Jigawa ta inganta harkokin kasuwanci -In ji Sarkin Kasuwar Shuwarin

Tura wannan Sakon

Daga Jabiru Hassan

Sarkin kasuwar Shuwarin da ke yankin qaramar hukumar Kiyawa jihar Jigawa Alhaji Muhammadu Shuwarin, ya ce ko shakka babu gwamnatin jihar tana qoqari wajen bunqasa harkokin kasuwanci da cinikayya a kasuwannin da suke fadin jihar, wanda kuma hakan ta sanya tattalin arziqi ke habaka kamar yadda ake gani a yau.

Ya yi tsokacin a yayin da Albishir ta yada zango a kasuwar, inda ya jaddada cewa, kasuwar Shuwarin tana da tsohon tarihi sannan ana sayar da dukkanin wani nau’in kayan amfanin gona da tufafi da dabbobi da sauran kayayyaki da muke amfani da su a gidaje na gargajiya ko na zamani.

Sarkin kasuwar ya sanar da cewa, ana zuwa kasuwar daga sassa daban-daban na fadin jihar da jihohi maqwabta har ma da qasashen da ke iyaka da jihar domin yin harkokin saye da sayarwa kamar yadda muke gani duk ranar Litinin wadda ita ce ranar da kasuwar  ke ci.

Daga nan sai ya yi nuni da cewa, kasuwar Shuwarin tana da girma, kuma akwai dukkanin abubuwan da ake buqata a kowace kasuwa musamman a yankunan karkara domin jin dadin yin hada-hadar yau da kullum ba tare da wata matsala  ba, inda daga qarshe ya yi bayanin cewa, nan gaba kadan kasuwar Shuwarin za ta zamo abar misali cikin sauran kasuwannin da ake da su a arewacin qasar nan.

Wani dan kasuwa da yaje kasuwar daga qasar Hadejia Malam Abubakar Aminu, ya ce “Kasuwar Shuwarin ta dade qwarai da gaske, sannan Allah ya sanya mata albarka duba da yadda ake ganin tana cika duk ranar litinin wanda hakan ya sanya ake mata zaton cewa, ita ce kasuwa mafi girma wadda take a karkara domin cinikayya”. In ji shi

Haka wani mai sana’ar sassaqa turame Malam Abdullahi Magaji, ya ce ko shakka babu sarkin kasuwar Shuwarin Alhaji Muhammadu ya na qoqari wajen tabbatar da cewa, kasuwar tana cikin yanayi mai kyau rani da damuna wanda ‘yan kasuwa ke alfahari da shugabancin sa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *