Gwamnatin Kano, a biya tsofaffin kansiloli hakkokinsu -Garzali Dogo

Garzali Dogo
Daga Abdullahi Sani Doguwa
Kungiyar tsofaffin kansilolin kananan hukumomin jihar Kano 44 na shekarar 2018 zuwa 2021 ta yi kira ga gwamnatin jihar, karkashin jagorancin gwamna, Dokta Abdullahi Umar Ganduje da ta taimaka ta cika alkawarinta na biyan tsofaffin kansilolin hakkinsu da suka karkare mulki a shekarar 2021.
Mai magana da yawun kungiyar kansilolin, tsohon kansila daga mazabar Unguwa Uku karamar hukumar Tarauni, Garzali Abdulrahman Dogo, shi ne ya yi koken ga gwamnatin, a madadin sauran kansilolin cikin hirarsa da manema labarai a ranar Asabar makon da ya gabata.
Garzali Dogo ya yi furucin cikin damuwa, ya ce, kungiyar kansilolin ta bi matakai iri daban-daban na ganin gwamnatin ta biya su hakkinsu, masamman ta hanyar zama da masu ruwa- da-tsaki kan sha’anin siyasar yau da kullum na jihar, tare da shiga kafafen watsa labarai, domin ganin an biyasu hakinsu, amma har kawo yanzu babu wani albishir daga gwamnatin, a cewar Garzali Dogo.
A cewarsa, la’akari da halin da kungiyar ta su ke ciki a halin yanzu, kamata ya yi gwamnatin ta yi dube na tsanaki, wajen ganin ta share masu hawaye masamman a daidai gabar ta tunkarar zaben shekarar 20 23.
Daga bisani hon. Garzali Dogo, ya yi addu’ar fatan alheri ga kasa dama jihar Kano, na kara samun wanzazzan zaman lafiya.