Gwamnatin Kano, a taimaka wa masu sana’ar kaji -Alhaji Idris

sana’ar Kiwon kaji

Tura wannan Sakon

Alhussain daga Kano

Kamar yadda gwamnatin jihar Kano a karkashin gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje, ke taimaka wa manya da kananan kungiyoyi da ke jihar, yana da kyau suma masu sana’ar sayar da kaji da ke jihar ya tuna da su domin kai masu tallafi.

Kiran ya fito ne daga bakin shugaban riko na kungiyar masu sayar da kaji na jihar Kano da ke kasuwar Muhammadu Abubakar Rimi Alhaji Idris Muhammad a lokacin da yake zantawa da manema labarai.

Alhaji Idris Muhammad ya ce, wani abu kuma shi ne sana’ar ta na samar da aikin yi ga al’ummar jihar Kano, musamman matasa ya bayar da misali da cewa, bayan sana’ar fawa babu wani sana’ar da ya kai dimbin matasa irin kasuwancin sayar da kaji a fadin jihar Kano, sannan akwai wadanda suka kammala karatunsu tun daga sakandare har ya zuwa jami’a .

Kungiyar tasu ta na bayar da haraji ga gwamnatin jihar a duk lokacin da bukatar hakan ta taso, kungiyar tana da dangantaka mai kyau tsakaninta da hukumar lafiya.

Malam Idris Muhammad ya nuna matukar farin cikin sa yadda alokacin sa kungiyar ta ke kara samun bunkasa da ci gaba da yanzu ta kai ga har masallaci ake ginawa a kasuwar, sannan kuma ‘yan kungiyar sun ba shi hadin kai da goyon baya yana fatan hakan zai dore.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *