Gwamnatin Kano za ta dauki likitoci 56

Gwamna Abdullahi Ganduje
Daga Usman Gwadabe
Gwamnatin Kano ta fara shirye-shirye don daukar likitoci 56 a kokarinta na inganta bangaren kiwon lafiya a matakin farko na jihar.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar, Malam Maikudi Muhammad Marafa ya sanar aka raba wa manema labarai.
Sanarwar ta ce, a cikin jawabinsa lokacin da yake yi wa masu neman aikin a lokacin da suka fara daukar jarabawar nuna kwarewa, Sakataren zartarwa na hukumar, Dakta Tijjani Hussain, ya bukaci masu neman su shirya kan kalubalen da ke gabansu.
Ya kara da cewa, za a horar da masu neman aikin da suka yi nasara a bangaren shugabanci da adana bayanai da kuma ayyukan kula da lafiya a matakin farko.
Don haka ya umarce su da su jajirce tare da sadaukar da kai lokacin da suka samu nasarar zama ma’aikatan hukumar.