Gwamnatin Kano za ta tallafa wa masu sana’ar kifi -Yahaya Muhd

A Kano: Gwamnati ta yi alkawarin kulawa da marayu

A Kano: Gwamnati ta yi alkawarin kulawa da marayu

Tura wannan Sakon

Alhussain Daga Kano

Gwamnatin jihar Kano, karkashin gwamna Abdullahi Umar Ganduje, na bai wa masu sana’ar kifi (kawara) na jihar Kano cikakkiyar hadin kai da goyon baya, kamar yadda yake bai wa sauran kungiyoyi da ke jihar.

Bayanin haka ya fito ne daga bakin shugaban kungiyar da ke kan hanyar Galadima, a Kano, Alhaji Yahaya Muhammad, a lokacin da yake zantawa da jaridar Albishir.

Alhaji Yahaya Muhammad, ya ce, hatta hukumar KAROTA da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro suna ba su hadin kai, saboda haka suna godiya sosai a

kan wannan tafiya da suke yi tare. Shugaban ya kara da cewa, sana’ar kifi kawara tana samar da aikin yi ga al’ummar jihohi dabandaban musamman matasa. Duk wanda ya zo da safe zai tabbatar da haka, inda ya kara da cewa, sanar ta fi kankama ne a lokacin da ruwan sama ya zo karshe .

Ya kuma yi amfani da wannan dama wajen kira ga masu sana’ar da su kara sanya tsoron Allah da kuma kwatanta gaskiya da amana, sannan su kasance masu tsaftar jiki da kuma abin da suke sayarwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *