Gwamnatin Katsina, a samar da mudu da sikeli -Alkalin-Alkalai

A Katsina: Shirin basda ya inganta ilimi a jihar

A Katsina: Shirin basda ya inganta ilimi a jihar

Tura wannan Sakon

Daga Muawuya Bala Idris, Katsina

Alkalin Alkalai na jihar Katsina, Khadi Muhammed Abubakar ya yi kira ga gwanatin jihar da ta samar da Mudu da Siketi na bai daya a jihar. Khadi Abubakar ya yi kiran a wajen kaddamar da mambobin Da’awah na shiya-shiya a karkashin hukumar daukaka shari’ ar Musulunci.

Ya ce, samar da samfurin Mudu da Siketi na bai daya zai kawo samar da adalci wajen kasuwanci a jihar. Khadi Abubakar ya hori mambobin kwamitin Da’awah da su yi aiki wajen tabbatar da bin dokokin Ubangiji tare da daukaka addinin Musulunci a fadin jihar.

Ya ce, kaddamar da su, ya yi daidai da dokar da ta kafa hukumar daukaka addinin Musulunci a jihar. Ya gode wa gwamnatin jihar Katsina a karkashin jagoranci Aminu Bello Masari wajen taimaka wa hukumar.

Tun farko, babban Jojin jihar Katsina, mai sharia Musa Danladi Abubakar ya yi kira ga mambobin da su yi aiki bisa gaskiya da rikon amana. Mai sharia Danladi ya tunatar da su cewa, aikinsu yana da muhammanci a addinin Musulunci, yana butakar hakuri da juriya.

A jawabin Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Sarkin Usman yaba wa hukumar daukaka addinin Musulunci ta yadda take tafiyar da ayyukanta.

Sarkin Katsina, Kabir Wanda ya samu Wakincin tsohon Alkalin Alkalai na jihar, Ahmed Batagarawa ya kaddamar da kwamitocin Da’awahh a shiya guda 7. Shiyoyin sun hada da shiyyar Daura, Dutsin-ma, Funtua, Kankia, Katsina, Malumfashi, da Mani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *