Gwamnatin Sakkwato: A dauki matakan kara yawan jami’an tsaro a Isa –Danbuga

Governor Aminu Tambuwal
Musa Lemu Daga Sakkwato
An yi kira ga gwamnatin jihar Sakkwato da ta mayar da hankalinta kacaukan a garin Isa, domin tabbatar da sanya kwararran matakai kan tsaro.
Daukar matakin ya zama wajibi ganin yadda al amuran tsaro ya tabarbare a yankin a inda yan ta’addan suke cin karansu ba babbaka.
Wannan kira ya fito ne daga wajen shugaban karamar hukumar Sabon Birni, Alhaji Jelani Danbuga a yayin da yake zantawa da manema Labarai a Sakkwato kan tabarbarewar tsaro a garin Isa.
A yayin da yake bayani ga manema labarai ranar Talatar da ta gabata, shuga
ban ya ce, ‘yan ta’addan suna cin karansu ba babbaka a garin Isa, musamman a cikin kauyukan Gazau da Lugu kazalika da garin Modaci a inda a kullum al‘ummar wadannan yanki suke cikin zulumi da tashin hankali.
Jelani Danbuga ya tabbatar cewa, jama’ar garin Isa sun san wadannan ‘yan ta’adda domin kuwa tare dasu suke mu’amula a kullum, musamman ta fuskar harkokin kasuwancinsu na yau da kullum.
Ya ce, ya kamata gwamnati ta tashi tsaye domin magance ta’addanci ta fuskar kara yawan jami’an tsaro, domin cim ma nasarar murkushesu ganin yadda suka yi katutu a wannan yanki.
Alhaji Danbuga ya bayyana cewa, a halin yanzu an sami sa’ido sosai a garin Sabon Birni, bisa dalilin samun kwararrun tsaro musamman a garuruwan Burkusuma Sabon Birni da Adabawa kazalika da kauyen Tsaburawa.
Shugaban karamar hukumar ya ce, wadannan ‘yan ta’adda suna fitowa ne daga garin Isa su zo garin Sabon Birni su aikata barna su koma garin Isa su boye.
Ya ce, bisa dalilin haka ya yi kira da kakkausar murya ga gwamnati ta samar da karin sojoji tare da ba su kayan aiki, domin su fuskanci wadannan azzalumai dake boyo a garurruwa daban-daban ciki har da kauyen Sakiru.
Daga karshe, Alhaji Jelani Danbuga ya tabbatar cewa, a yanzu babu yan gudun hijira a garin Sabon Birni da kewaye kowa ya koma mahaifarsa na haihuwa.