Gyara dokokin zaBe, ba matsalolin Nijeriya ba -Uba Garkuwa

Tura wannan Sakon

Labari Isa A. Adamu Daga Zariya

An bayyana matakin da majalisar tarayya ta Dauka na yin gyara a dokokin zaBe a Nijeriya da cewar ba shi ne matsalolin da suka dabaibaye zaBuBBuka da ake yi a Nijeriya ba da ake ganin yin gyara wasu ci gaba aka samu da zai zama silar samun zaBe nagari ba.

Tsohon Dan takarar majalisar tarayya a KarKashin jam’iyyar PDP a shekara ta 2007 KarKashin ja’iyyar PDP, Alhaji Uba Garkuwa, ya furta haka, a lokacin da ya zanta da wakilinmu, kan gyare – gyaren da majalisar tarayya ta yi da za a fara ganin gyaran a zaBen shekara ta 2022.

Alhaji Uba Garkuwa ya ci gaba da cewar, babbar matsalar zaBe a Nijeriya shi ne rashin bin dokokin zaBe da ake yi a duk wani zaBe da ake yi a Nijeriya, sai dai, a cewarsa, a gudanar da zaBen da waDanda ma su mulki ke so, su ke samun nasara ko da ma su yin zaBe a Nijeriya bas a so.

Alhaji Garkuwa ya Kara da cewar, duk wani mai mulki baa bin da yak e sa wa a gabansa a lokutan zaBe, sai gudanar da zaBe yadda zai yi wa waDanda suke mulki daDi, ta aje tsare – tsaren zaBe gefe guda, a Karshe ba tare da tunanin matsalolin da ka iya tasowa ba, bayan an fitar da zaBen da ba shi ne al’umma suka yi ba. A game da batun da ko wane mai matsayin siyasa a duk madafun iko, dole su sauka kafin zaBe, Alhaji Uba Garkuwa ya ce, in har wannan doka ta yi amfani akafin zaBen shekara ta 2023, babu ko shakka, za a ga zaBe nagari da kowa zai sami natsuwa da zaBuBBukan da aka yi. Ya Kara da cewar, in wannan doka ta sami karBuwa babu waDanda za su ji daDin gudanar da ayyukansu na yin zaBe kamar hukumar zaBe ta Kasa, a duk zaBe ma su madafun iko ke sa Kafa su ture duk wani sakamakon zaBen da ba su sami nasara a kan sa ba.

A tsokacin da Alhaji Uba Garkuwa ya yi na dalilan da mafiya yawan waDanda ke madafun iko ba sa son sauka daga kujerunsu da suke kai, ya ce, sun san in har suka sauka kafin zaBe, alamu a yau, a cewarsa, sun nuna, mafiya yawansu, babu wanda zai koma kan kujerarsa, a dalilin rahin Karfin mulkin da ya ke ba shi a hannunsu.

A dai zantawarsa da wakilinmu ya yi tsokaci kan yadda, a cewarsa za a sami canji a zaBen shekara ta 2023, inda jam’iyyar NNPP za ta zama mai jan ragamar Nijeriya, ba wai arewa kai ko kuma wani sashi na Nijeriya, musamma, kamar yadda Alhaji Uba Garkuwa ya ce in an dubi yadda fitattun ‘yan siyasa suka dunKule a jam’iyyar NNPP.

A kan haka, Alhaji Garkuwa ya nunar da cewar, jam’iyyun da suke Nijeriya, musamman waDanda suka riKe madafun iko a baya, ya tabbatar da cewar, ‘yan Nijeriya sun gwada su, amma ba su kai su tudun – mun – tsiri ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *