Gyaran matatun-mai: Gwamnati ta kashe Naira biliyan 100 -Mele Kyari

Malam Mele

Malam Mele

Tura wannan Sakon

 Daga Mahmud Gambo Sani

Kamfanin albarkatun mai na Nijeriya NNPC ya ce, ya kashe Naira biliyan 100  wajen farfado da matatun mai da ba sa aiki a shekarar da ta gabata.

Rahoton da kamfanin ya gab­atar ya nuna cewa, a kowane wata yana kashe fiye da Naira biliyan 8 wajen kula da matatun man.

‘Yan Nijeriya sun dade suna korafi a kan yadda matatun ba sa iya aiki kamar yadda ake bukata, idan aka yi la’akari da dimbin kudaden da ake kashewa a kansu.

Shugaban rukunin kamfanonin na NNPC, Mele Kyari, ya ce, an rufe matatun man ne saboda sun gaza gu­danar da ayyukansu kamar yadda ya ake bukata.

Idan za a iya tunawa, a babban taron da kungiyar editocin Nijeriya ta gudanar a Abuja cikin watan Ok­toba, 2021, Mele ya bai wa ‘yan Ni­jeriya tabbacin cewa, matatun man za su fara aiki a cikin watan Disamba 2021, inda har Albishir ta buga kanun babban labarinta da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *