Haba Sha’aban Sharada, mene ne siyasa?

Daga Kwamrade Ibrahim Abdu Zango
Na fahimci cewa, Alhaji Sha’aban Ibrahim Sharada mutum ne wanda ya yi aikin Jarida watau kacokan shi dan jarida ne a wani gidan Rediyo a nan Kano.
Wani hukuncin Allah, kusan ya sami wata daukaka wacce ta zama har yazo kusa da fadar shugaban Dasa Muhammadu Buhari.
Gaskiyar lamari Sha’aban Ibrahim Sharada dan siyasa ne, amma karami wanda ya shigo da kafa biyu, kuma cikin nasara. Hakika kamar yadda na gane siyasa aba ce wacce ta zama ana yi ne shekara da shekaru, kafin zama dan siyasa na din-din-din. Malam Sha’aban Ibrahim Sharada duk da yake karamin dan siyasa ne, amma gaskiya shi da idan ana gadon siyasa to ya gaje ta, domin nasan Abbansa Allah Ya jikansa, dan siyasa ne kuma cikakken malami. Abokin siyasar Marigayi Muhammad Abubakar Rimi, watau shi Abban Sha’aban Ibrahim Sharada a unguwar Zango yake, kuma malami ne kwarai da gaske, kuma a wurina dancuwane kuma malami na.
Ka ga ashe shi Sha’aban Ibrahim Sharada ya sami tarbiyya sosai kocda yake dai sun tashi daga unguwar Zango sun koma unguwar Sharada kuma watakil shi ne dalilin da yasa Sha’aban Ibrahim Sharada yake amsa cewa, Sha’aban Sharada. Ban san ko cewa, Sha’aban ya je Jami’a ba, amma dai ya yi kos din “Mass Communication” watau na kasance wa dan jarida wanda ya yaiki a “Freedom Radio” wacce take a unguwar Sharada kuma watakila ta haka ne ya sami damar shiga daf da daf da fadar shugaban dasar Nijeriya, wannan babbar falala ce, wacce ta kasance abar bida.
To shigar wannan bawan Allah cikin wannan falala, ita ce ta ba shi damar ganin muhimman mutane masu fada a ji, kuma sun ba shi karfin gwiwa ta samun ababe masu nauyi kwarai da gaske saboda haka watakila ta haka ne sanadiyyar shigarsa siyasar. Gaskiya shi Sha’aban Ibrahim Sharada ba shi kadai suka zo neman zama dan takara ba, kuma a jam’iyyar APC, jam’iyyar shugaban kasar Nijeriya Alhaji Muhammadu Buhari.
Akwai wani wai shi Kawu wanda shima ance yayi aiki a ofishin mataimakin shugaban kasa wato Maigirma Osibanjo. Hon. Hafiz Ibrahim Kawu Tarauni ya tsaya zabe, akwai dayan kuma wanda ya tsaya daga Dala kuma shi baiyi sa’a ba domin bai ci zaben ba. To cikin wadannan mutane uku babu wanda yayi fice da surutai barkatai kamar shi wannan yaro Sha’aban Ibrahim Sharada, tun kafin zamansa dan majalisar tarayya ya shiga rudani da yawan gaske, kuma kawai sai muka fahimci cewa sabon hannu ne shi a siyasa kuma irin wannan hali ba kasafai yake da yawan zama abin kirki ba.
Hon. Sha’aban surutu barkatai batawa mutum abubuwan kirki yake, kuma gaskiya babu alheri a cikinka, kuma yana kassara mutuncin mutum. A takaice dai Sha’aban Ibrahim Sharada a bisa tunani na, a hankali yake so ya koma jam’iyyar PDP domin take-takensa na zargin gwamnatin Kano wacce ta tsaya masa babu dare, babu rana domin taga ya sami damar darewa akan kujerar da yake kai, duk da cewa gaskiya shekarunsa bai kai ya dare kujerar ba, saboda dalilin da yanzu ya bayyana a kasa, kususan na nuna ko ubali da yake yi da kuma raina shugabancin jam’iyya wacce ya dare kan kujerar da yake a yanzu. Naga har wai Danliti Kwamanda ya shiga jirgin caccakar gwamnatin Kano wanda a baya yake ta sukar shi wannan yaron dan siyasa!
Shi Sha’aban Ibrahim Sharada, komai abin da yake jin yana da shi, to su Kwamandan cin zarafin mutane suka iya, to fa za’a iya shiga cikin ni ‘yasu. Sha’aban Ibrahim Sharaza akwai kyakkyawar fahimtar cewa yana da wata aba wacce bature yake kira “Bright Future”, saboda haka rikice-rikice ba naka bane, kuma kada ka ringa batawa da jama’a, domin wasu masu baki da kunu suke zuga ka, ka ke fadin ababe marasa manufa. Gaskiya ba ruwa nada cewa ina goyon bayan dayanku, illa kawai ka tsaya a matsayinka na yaro inda a kance yaro tsaya matsayinka, kada zancen ‘yan duniya ya rudeka.
Nasan san da cewa duniya rumfar kara – ni – Audu – na sagale kafa, radda zata kife ban fargaba.
Kada ka zama Dan Dufanni yaya na falo mana.
Mu kwana a nan. Kwamrade Ibrahim Abdu Zango Kano, Nigeria – 08175472298