Hada Ganduje, Tinubu a takara zai haifar da alheri -Kungiyoyin matasa

Tura wannan Sakon

Daga Jabiru Hassan

Kungiyoyin matasa a jihar Kano sun bayyana cewa, salon siyasar gwamnan jihar, Dokta Abdullahi Umar Ganduje za ta samar da ci gaba mai albarka a fadin kasarnan, duba da yadda jihar Kano ta zamo abar misali bisa jagorancinsa.

A cikin wata sanarwa da jerin kungiyoyin matasan suka fitar da yammacin ranar Talatar da ta gabata, sun jaddada cewa, gwamnan jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje, ya san dimokuradiyya sosai, duba da yadda ya dade a fagen siyasa da harkar mulkin al’umma.

Shugaban gamayyar kungiyoyin matasan, Kwamared Mustapha Umar Tallo Gwarzo, wanda kuma shi ne jagoran matasan Kano ta Arewa, ya sanar da cewa, matasan jihar Kano sun gamsu da yadda gwamna Ganduje yake tafiyar da jagoranci da irin salon shugabancinsa, tun daga shekara ta 1999, lokacin da ya zamo mataimakin gwamnan Kano.

Ya ce, “Babban abin da muka sanya a gaba yanzu shi ne, hada kan dukkanin kungiyoyin matasan jihar Kano, domin yin tafiya da murya daya wajen ganin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ci gaba da bayar da gudummawarsa wajen ci gaban Nijeriya, ta yadda kowa zai amfani ribar dimokuradiyya ta kowane fanni”.

Dangane da maganar daukar mutumin da zai yi wa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu mataimaki kuwa, Kwamared Mustapha Umar ya bayyana gwamna Ganduje a matsayin wanda ya cancanci yi wa Tinubun mataimaki, saboda kwarewarsa a sha’anin mulki da tafiyar da jagoranci a tsari irin na dimokuradiyya mai riba.

Mustapha ya nunar da cewa, maganar kada a hada Musulmai su yi takara ba shi ne abin dubawa ba, amma babban abin bukata shi ne, mutanen da za su yi wa kasa aiki bisa kishi da samar da managarcin ci gaba da kuma hada kan kasa ta kowane vangare, tare da yin kira ga dan takarar shugaban kasa, Bola Tinubu, da daukacin masu ruwa-da-tsaki a cikin jam’iyyar APC, da su ayyana gwamna Ganduje a matsayin wanda zai kasance mataimakin shugaban kasa a zaven 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *